
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya tabbatar wa Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana tare da kafafen yaɗa labarai kuma za ta cigaba da kare ƴancin tofa albarkacin baki a ƙasar.
Shettima ya faɗa haka ne a lokacin da shugabannin NUJ suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce, Shugaba Tinubu ya daɗe yana goyon bayan aikin jarida tun kafin ya hau mulki, don haka ba zai taɓa kassara kafafen yaɗa labarai ba.
Ya bayyana cewa, aikin jarida na da muhimmanci wajen riƙe gaskiya da tabbatar da adalci, inda ya kwatanta shi da aikin shari’a wajen kula da shugabanci.
A nasa jawabin, Shugaban NUJ, Alhassan Abdullahi ya roƙi gwamnati da ta cire dokokin da ke matsa wa ‘yan jarida da kuma samar da tallafin horo da rance ga kafafen labarai.
Ya kuma buƙaci a kafa dandalin haɗin-kai tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai don kauce wa yaɗuwar bayanan ƙarya acikin al’umma.
