Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya rantsar da sabbin Kwamishinoni uku da kira a gare su da a ko da yaushe su yi aiki da gaskiya da riƙon amana.
Ya ja hankalinsu da su ɗauki muƙamansu a matsayin nauyin amanar jama’a, ba wata hanya ta azurta kan su ba.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a fadar gwamnati ta Katsina, inda manyan jami’an gwamnati, sarakuna da ‘yan uwa na waɗanda aka naɗa suka halarta.
Sabbin kwamishinonin sun haɗa da Hon. Yusuf Suleiman Jibia, Hajiya Aisha Aminu, da Injiniya (Dr.) Sirajo Yazid Abukur.
Gwamna Raɗɗa ya yabawa Hon. Yusuf Suleiman Jibia a matsayin tsohon ɗan siyasa mai ƙwarewa wanda ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati. Ya kuma bayyana Hajiya Aisha Aminu a matsayin abin koyi ga mata a sha’anin gwamnati da kasuwanci, sakamakon irin rawar da ta taka a matsayin shugabar farko ta KASEDA.
A kan Injiniya Sirajo Abukur, Gwamnan ya ce naɗin sa ya nuna ƙudirin gwamnati na baiwa matasa dama da tabbatar da adalci ga ƙaramar hukumar Rimi wadda ba ta taɓa samun kwamishina ba tun bayan dawowar dimokuraɗiyya.
Ya buƙaci sabbin kwamishinonin da su yi aiki da tawali’u, gaskiya, da himma domin ci gaban jihar.
Har ila yau, gwamna Dikko Raɗɗa ya rantsar da sabbin Manyan Sakatarori takwas a jihar.
