Remi Tinubu ta ƙaddamar da cibiyar dijital a Zamfara

Spread the love

Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau

Uwargidan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da cibiyar hada-hadar karatu ta dijital watau E-learning Library Center na miliyoyin Naira a yau Alhamis a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Uwargidan shugaban ƙasar kuma shugabar shirin sabunta ƙasa ta bayyana cewa an kuma kafa cibiyoyin a jihohi 10 domin bunƙasa fasahar E-Learning na dijital a tsakanin ɗalibai.

Sen. Remi Tinubu wadda ta samu wakilcin uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal a wajen taron, ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta ƙasa (NITDA) aka kafa cibiyoyin goma.

“Wannan aikin ba wai na fasaha da na’ura mai ƙwaƙwalwa ba ne kawai, yana da nufin ƙarfafa matasanmu, tare da daidaita rarrabuwar kawuna da buɗe sabbin ƙofofin ilimi da ƙirƙire ƙirƙire ga mutanen Zamfara da sauran su.” Ta ce

Ta jaddada buƙatar da ƙara mai da hankali kan ilimin yara mata, inda ta jaddada cewa a wannan zamani, samun kayan aikin koyon karatu na Digital tana da matuƙar tasiri.

“Ta hanyar wannan ɗakin karatu, ɗalibai, malamai, masu bincike da sauran jama’a za su sami damar yin amfani da duniyar bayanai, don samun albarkatu da dama a hannunsu”.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana sabon shirin da Sanata Oluremi Tinubu ta yi a matsayin wani shiri na tallafawa ilimi, ƙirƙire ƙirƙire, da ci gaban zamantakewa.

Ta yabawa ma’aikatar sadarwa, ƙirƙire ƙirƙire da tattalin arziki na zamani ta tarayya da hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta ƙasa (NITDA) bisa gudanar da wannan aiki a jihar ta Zamfara.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yabawa gwamnatin jihar Zamfara, ƙarkashin jagorancin Mijin ta, Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar gwamnatinsa na inganta fannin ilimi a jihar Zamfara.

“Ga al’ummar Zamfara musamman ɗaliban mu da malamanmu, ina roƙon ku da ku yi amfani da wannan wurin da kyau “. Ta ce

A jawabin maraba, Sakatariyar dindindin ta ma’aikatar ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Zamfara, Hajiya Maryam Shantali, ta bayyana cibiyar koyar da ilimin yanar gizo a matsayin abun maraba inda ta bayyana cewa cibiyar za ta bunƙasa ilimin zamani a jihar.

A nasa jawabin, DG/CEO National Information Technology Development Agency(NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi, wanda Ismail Ahmad ya wakilta ya bayyana cewa cibiyoyin karantarwa ta yanar gizo za su samar da damammaki na bunƙasa kasuwanci.

By ukarofi