Za a yi gumurzu a zaɓen 2027 – Kwankwaso

Spread the love

*A shirye muke mu yi haɗaka, inji shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar kujerar Shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi hasashen cewa zaɓen 2027 zai kasance mafi tsanani a tarihin dimokuraɗiyyar Nijeriya, kamar yadda ya bayyana cewa jam’iyyarsa a shirye take ta ƙulla ƙawance da sauran jam’iyyun siyasa ciki har da shugaban ƙasa Bola Tinubu da Peter Obi na jam’iyyar Labour.

Da yake magana a wata hira da BBC Hausa da Blueprint Manhaja ta sa ido, Kwankwaso, wanda a kwanan nan ya cika shekaru 69 a duniya, ya ce jam’iyyar NNPP a shirye take ta haɗa kai da duk wata jam’iyyar siyasa ko kuma wani mutum da yake da ra’ayinsa na ganin Nijeriya ta samu ci gaba da kuma sadaukar da kai ga rayuwar talakawa.

Sai dai ya nanata cewa duk wani haɗaka ko ƙawance dole ne a yi shi bisa mutunta juna, fayyace fa’ida, da manufa guda, musamman cigaban talaka.

“Muna shirye ga kowa, ko APC, PDP, ADC, Jonathan, ko Peter Obi. Idan mun gamsu da cancantar su da amincin su, za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe don samun nasara,” inji Kwankwaso.

“Amma duk wanda muke ƙawance da shi dole ne mu himmatu wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, idan har suka kasa cimma burinmu, ba za mu ci gaba da ƙawance da shi ba, abin da muke nema shi ne mai sauƙi da ya kamata talakawa su amfana, a ilmantar da matasa, a kuma inganta tsaro,” inji shi.

Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP da ta tsayar da ‘yan takara a dukkan jihohin ƙasar nan a zaɓen 2023, ta zama wata jam’iyya ta ƙasa da za ta iya yin tasiri a alƙiblar siyasar ƙasar nan.

Ya tuna cewa a watan Satumba, ya yi nuni da yiwuwar jam’iyyar NNPP ta yi aiki tare da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki amma ya jaddada cewa dole ne irin wannan matakin ya zo da kimar gaske ga tsarin jam’iyyar NNPP da ‘yan takara.

“Idan kuna neman mu koma APC, to ku gaya mana abin da NNPP za ta samu, muna da ‘yan takarar gwamna a dukkan jihohi da cikkaken tsare-tsare a faɗin ƙasar, me za ku ba su idan muka shiga? Ya tambaya.

Tsohon Ministan Tsaron ya kuma yi wa jiga-jigan siyasar Nijeriya kaca-kaca, inda ya zarge su da yin watsi da wahalhalun da talakawa ke fuskanta yayin da suke zaune a Abuja.

“Ana kashe mutanenmu a Sokoto, Kebbi, Zamfara, da wasu sassan Kaduna, waɗanda aka ƙashen talakawan ƙasa ne, jiga-jigan sun gudu zuwa Abuja, inda suke zaune a gidajen alfarma, suna tuƙa motoci masu tsada, suna arzurta kansu da dukiyar jama’a,” inji shi.

“Suna yi kamar ba za a taɓa su ba, amma ina da yakinin cewa Allah zai yi musu hukunci daidai da abinda suka aikata.”

A zaɓen 2027, Kwankwaso ya yi hasashen fafatawar za ta fi zafi da rashin tabbas, inda ya ce ‘yan Nijeriya a yanzu sun fi sanin siyasa da kuma ƙudurin canza yanayinsu.

“Na yi imanin cewa zaɓen 2027 zai fi tsanani. Yanzu mutane sun fi sani, sun fi damuwa, da kuma shiga tsakani, kowa na neman mafita saboda halin da ƙasar ke ciki,” inji shi.

“Godiya ga gidajen rediyo da kafofin sada zumunta, talakawa yanzu sun ƙara wayewa. Kuna iya ganin abubuwan da ba su taɓa faruwa ba a tarihin zaɓukan Nijeriya. Mutane ba za su sayar da ƙuri’unsu a wannan karon ba, suna son canji na gaske.”

By ukarofi