Jiga-jigan PDP na Arewa sun cimma matsaya kan Kabiru Turaki a matsayin shugaban jam’iyya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Ministan Harkokin Musamman da Dangantakar Gwamnatoci, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa bayan cimma matsayar haɗin kai tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar daga arewacin ƙasar.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya sanar da fitowar Turaki a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a Abuja daren Laraba, 22 ga Oktoba, 2025.

An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai zurfi da aka yi tsakanin shugabannin jam’iyyar daga arewa, domin ƙarfafa haɗin kai da daidaiton cikin gida kafin babban taron jam’iyyar da ke tafe a shekarar 2025.

Taron ya samu halartar fitattun jiga-jigan PDP, ciki har da Umar Damagum (mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar), Gwamna Dauda Lawal (Zamfara), Bala Mohammed (Bauchi), da Ahmadu Fintiri (Adamawa).

Sauran tsofaffin shugabanni da suka halarci taron sun haɗa da Far. Jerry Gana (tsohon Ministan Yaɗa Labarai), Bukola Saraki (tsohon Shugaban Majalisar Dattawa), Ibrahim Shekarau da Ahmed Makarfi, tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna.

Sanata Abba Moro, shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, shi ma ya halarci taron.

Zaɓen Kabiru Turaki a matsayin sabon shugaban PDP na da nufin haɗa kan jam’iyyar da kuma shirya ta tsaf domin fuskantar zaɓen shekarar 2027, wanda ake sa ran zai zama wani babban gwagwarmaya a siyasar ƙasar.

By ukarofi