Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) sun samu babbar nasara kan ’yan ta’adda, inda suka halaka aƙalla ’yan ta’adda 62 ciki har da shahararrun kwamandojin ISWAP guda biyar, bayan sun fatattake a hare-haren da aka kai musu a sansanonin soji daban-daban a jihohin Borno da Yobe — abin da aka bayyana a matsayin babban nasarar soja mafi girma a shekarar 2025.
Hare-haren da suka faru ne a lokaci guda tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na safe a ranar Alhamis, inda mayaƙan ISWAP suka aaddamar da gagarumin hari kan sansanonin soji a Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko, cikin Sectors 1 da 2 na yankin hazin gwiwar ayyukan tsaro.
A wata sanarwa da Lt.-Col. Sani Uba, jami’in hulza da jama’a na rundunar, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce dakarun sun nuna jarumta da ƙwarewa wajen mayar da martani, inda suka tarwatsa ’yan ta’addan tare da jawo musu mummunar asara.
“A kowane lokaci, dakarunmu sun tsaya kai da fata, sun yi fafutuka cikin jarumta, sun kuma fatattaki hare-haren tare da jefa ’yan ta’addan cikin mummunar asara,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, haɗin kai tsakanin sojojin ƙasa da rundunar sama, tare da kai farmaki cikin daidaito, ya taimaka wajen kashe ’yan ta’adda sama da 62, yayin da wasu da dama suka gudu da munanan raunuka.
An kuma kwato bindigogi AK-47 guda 38, PKT guda 7, RPG 5, GPMG 2, gurneti da harsasai dubban, yayin aikin share wuraren.
Bayanan leƙen asiri sun tabbatar da cewa cikin waɗanda aka kashe akwai manyan kwamandojin ISWAP guda biyar:
Ari Kolo (Munzir Abbagajiri), Ya Muhammad (Dosula), Abu Aisha (Abba Gajiri), Hamzalah (ƙaid a Gambo Gege da Faruk), da Abu Rijal (Dosula).
Rahotanni sun nuna cewa waɗannan kwamandojin sun kasance masu tsara dabaru da kai hare-hare kan sansanonin soji, tare da shirya bam-bam na IED da jiragen leƙen asiri, a yankin Arewa maso Gabas.
Sojojin leƙen asiri sun bayyana cewa mutuwarsu ta girgiza tsarin ISWAP, domin su ne manyan masu tsara dabarun kai farmaki daga ɓangarori daban-daban da RPG, bindigogin harbo jirgi, da ƙungiyoyin ƙunar baƙin wake.
Sai dai hare-haren nasu sun gamu da martani mai ƙarfi daga sama da ƙasa, wanda ya ɗauki fiye da awanni huɗu, inda sojoji suka fatattaki ’yan ta’adda a Dikwa, Katarko, Gajibo da Mafa. A Mafa dai, ’yan ta’adda sun yi nasarar shiga na ɗan lokaci, amma sojoji suka kora su bayan sun aone wasu motoci.
Kanar Uba ya ce kai farmaki daga sama cikin daidaito da goyon bayan na’urorin ISR ya bai wa dakarun rinjaye. Ya ce ana ci gaba da bin sawun ’yan ta’addan da suka gudu fiye da 70, yayin da rundunar sama ke ci gaba da lura da su.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ’yan ISWAP da suka kai hari a Dikwa da Gajibo sun fito daga yankin iyakar Kamaru, yayin da waɗanda suka kai hari a Katarko suka fito ne daga yankin da ake kira Timbuktu Triangle — sanannen mafakar ’yan ta’adda.
