Majalisar Wakilai ta umarci a gyara hanyar Bida–Agaie bayan gobarar tanka ta kashe mutum 30

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta umarci Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya tare da Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) da su hanzarta gyara da faɗaɗa hanyar Bida–Agaie–Lapai–Lambata–Diko, bayan yawaitar gobarar tankokin mai da ke faruwa a yankin.

Wannan mataki na Majalisar ya biyo bayan gobarar tankar mai da ta afku a yankin Essa, inda rahotanni suka ce sama da mutum 30 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 40 suka ji mummunar rauni.

Majalisar ta kuma umarci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ƙarfafa matakan tsaro da binciken lafiyar motocin ɗaukar mai da manyan motoci, domin rage aukuwar irin waɗannan bala’o’i.

Haka kuma, Majalisar ta nemi Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta samar da kayan tallafi da kulawar lafiya ga waɗanda gobarar ta rutsa da su da iyalansu.

Bugu da ƙari, an umarci Kwamitin Hada-hade na Ayyuka, FERMA, FRSC da Harkokin Kuɗi da su gudanar da cikakken bincike kan halin da hanyar ke ciki da kuma matsayin yarjejeniyar da aka taɓa yi da kamfanoni kafin yanzu.

Wannan ƙuduri ya biyo bayan motsin da ɗan majalisa mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha, Hon. Saidu Musa Abdullahi, ya gabatar a zaman majalisar ranar Laraba.

Abdullahi ya bayyana cewa gobarar da ta auku a ƙauyen Essa ba ita ce ta farko ba, domin akwai jerin manyan haɗurra da suka riƙa faruwa a wannan hanya cikin watanni da suka gabata, wanda hakan ke janyo asarar rayuka, lalacewar dukiya da gajiyar masu zirga-zirga.

Ya kuma tunatar da cewa aikin gyaran hanyar na daga cikin shirin Road Infrastructure Taɗ Credit Scheme, tsarin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) wanda ke bai wa kamfanoni damar amfani da kuɗin haraji wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.

ɗan majalisar ya koka da cewa watsi da wannan hanya mai matuƙar muhimmanci ya haifar da cunkoso, lalacewar kaya, asarar lokacin aiki da wahala ga matafiya da mazauna yankin.

By ukarofi