Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ta sulhu da ’yan bindiga ba, kuma ba za ta biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane ba — yana mai kira ga al’ummar jihar da su ɗauki mataki na kare kansu daga hare-haren da ke ƙaruwa a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ziyarar jaje da ya kai garuruwan Rijau da Magama a yankin Kontagora, inda ’yan bindiga suka yi mummunan ta’adi a kwanakin baya.
Da yake magana cikin fushi da takaici, Gwamna Bago ya ce lokaci ya wuce na nuna sassauci ga masu laifi, domin biya musu kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa su ne wajen ɗaukar mutane a matsayin hanyar kasuwanci.
“Mun kai matakin da dole jama’a su tashi tsaye su kare kansu. Ba za mu biya fansa ba. Idan muka fara biya, za su bude kasuwa a kanmu. Wannan lamari ya zama kamar yaƙi, dole mu tashi gaba ɗaya mu fuskance shi,” inji gwamnan.
Ya ƙara da cewa, ’yan jihar Neja suna da cikakken ikon doka na kare rayukansu da dukiyoyinsu, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta sake lamunta da rashin tsaro da ta’addanci ba.
“Mun kewaye da makiya, amma ba za mu miƙa wuya ba. Kundin tsarin mulki ya ba mu ikon kare kanmu, kuma wannan ne za mu yi. Babu ja da baya,” Bago ya jaddada.
Gwamnan ya bayyana hare-hare da korar jama’a daga gidajensu a matsayin abin kunya da rashin amincewa, sannan ya sanar da sabon shirin tsaro na ɗaukar sabbin mambobin rundunar haɗin gwiwa (JTF) har 10,000, domin su taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda a faɗin jihar.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin jaridu, Aisha Wakaso, ta fitar, Gwamna Bago ya kuma ayyana haramcin duk wasu ayyukan hakar ma’adinai a yankin Zone C na jihar — wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi takwas: Magama, Kontagora, Rijau, Wushishi, Mariga, Borgu, Mashegu da Agwara.
Ya bayyana cewa haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da rashin tsaro, yana zama mafaka da hanyar samun kuɗi ga ’yan ta’adda.
“Abin mamaki ne yadda ma’adinai ke shiga daji su yi aiki ba tare da wani ya taɓa su ba. Na umarci jami’an Civil Defence su kama duk wanda aka samu yana haƙar ma’adinai daga yau,” inji gwamnan.
Bago ya kuma tabbatar wa waɗanda suka rasa ’yan uwansu ko dukiyoyinsu sakamakon hare-haren cewa gwamnatinsa za ta tallafa musu — da kuɗin diyya, magani da taimakon gina gidaje ko sana’o’i.
Ya kammala da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin Jihar Neja, tana amfani da duk wata hanya da ta dace don kare rayuka da dukiyar jama’a.
