Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsadar gas ta kai ƙololuwa a Nijeriya, inda farashin kilogiram ɗaya ya kai N1,600, lamarin da ya tilasta yawancin iyalai komawa amfani da gawayi, garin katako da itace domin dafa abinci.
Rahotanni daga Blueprint sun nuna cewa yajin aikin da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Gas (PENGASSAN) ta shiga ya haifar da cikas ga harkar rabon iskar gas, wanda ya haddasa ƙarancin kayayyaki da tashin farashi a sassan ƙasar.
Yajin aikin na tsawon kwanaki uku ya katse rabon kayayyaki daga manyan kamfanoni kamar matatar Dangote, da kuma gyare-gyare a Nigeria LNG Train 4.
Sai dai masana tattalin arzikin makamashi sun ce matsalar ta daɗa tana taƙaita rayuwar mutane, musamman tun shekaru biyu da suka wuce, kuma yanzu ta kai matsayi mafi muni a watan Oktoba 2025.
Dr. Tunde Adeniyi, masanin tattalin arzikin makamashi, ya bayyana cewa dogaro da ‘yan kaɗan daga cikin masu samar da gas da kuma rashin tsare-tsare na gaggawa ne suka bar kasuwar cikin gida cikin rauni da fargaba.
“Wannan abin kunya ne. Gas muhimmin tushe ne na makamashi a cikin gida. Bai kamata gwamnati ta bari yajin aiki ko gyaran masana’anta su katse samar da shi ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, tsarin kasuwar gas na yanzu yana da sauƙin shiga hannun masu ƙulla farashi da ƙirƙirar ƙaranci ta hanyar dabarar kasuwa.
Binciken kasuwa ya nuna cewa farashin kwalban gas mai nauyin 12.5kg ya tashi daga N13,500 zuwa N22,000 cikin wata guda – ƙaruwa da kusar da kashi 63%.
A sassa da dama na ƙasar ciki har da Legas, an ga dogayen layuka a tashoshin gas, inda mutane ke tururuwar zuwa su cika silindar su kafin farashi ya sake hawa.
Yanzu haka iyalai da dama musamman a yankunan arewa da kudu maso gabas sun koma amfani da gawayi, garin katako da itace domin rage kuɗin dafa abinci.
