Obasanjo ya buƙaci shugabanni su zuba jari kan matasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce shugabanni da manyan jama’a suna da nauyin nuna gaskiya, amana da shugabanci mai nagarta ga matasan ƙasa, domin inganta makomar Nijeriya.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abeokuta yayin babban taron haɗuwar tsoffin ɗaliban kwalejin Royal College of Defence Studies (RCDS) na Birtaniya, reshen Nujeriya, inda ya gabatar da jawabi mai taken “ƙalubalen Matasan Duniya.”

A cikin jawabinsa, Obasanjo, wanda Farfesa Samuel Daramola ya wakilta daga Olusegun Obasanjo Leadership Institute — ya bayyana matashi a matsayin lokaci tsakanin ƙuruciya da balaga, lokacin da ake da kuzari, fata, mafarki da hangen nesa.

Ya ce, “A da, mu ma mun kasance matasa bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Duk da cewa duniya ba ta cika ba, akwai tsarin da ake bi, girmamawa ga dokokin ƙasa da ƙasa, da zaman lafiya da daidaito tsakanin manyan ƙasashe. Amma yau, matasa na fuskantar manyan ƙalubale a duniyar da ta rikice.”

Obasanjo ya yi gargaɗin cewa shugabanni su guji cinye albarkatun da ya kamata a bar wa al’umma ta gaba, tare da yin zuba jari mai ma’ana don amfanin nan gaba. Ya ce dole ne a haɗa matasa a cikin dukkan fannoni na rayuwa — daga gida zuwa kasuwanci da gwamnati.

Ya ƙara da cewa, “Matasanmu ba shugabanni ne na gobe kaɗai ba — shugabanni ne na yau. Ya zama dole a basu dama a tsarin jagoranci domin gina ƙwarewa ta shugabanci.”

Shugaban ƙungiyar tsoffin ɗaliban RCDS, Manjo Janar Oluwaseun Oshinowo (mai ritaya), ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara aiki shekaru takwas da suka gabata, kuma taron na bana na nufin tattauna batutuwan da za su taimaka wajen cigaban ƙasa.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama, wanda Darakta Abosede Awolola ta wakilta, ya yaba da muhimmancin taron wajen haɗa shugabanni masu hangen nesa daga sassan duniya. Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙuduri aniyar aiwatar da manufofin ƙasashen waje masu fifita ɗan ƙasa da bunƙasa tattalin arziki.

A nasa jawabin, Gwamna Dapo Abiodun na Ogun (wanda mai ba shi shawara kan tsaro, Olusola Subair, ya wakilta), ya bayyana cewa rushewar tarbiyyar iyali na daya daga cikin barazanar da ke hana cigaban ƙasa, tare da kira ga iyaye da shugabanni su gyara tunanin matasa zuwa ayyukan da ke da amfani.

An kafa makarantar Royal College of Defence Studies (RCDS) a shekarar 1927 a ƙasar Birtaniya domin horar da shugabanni a matakin dabarun tsaro da jagoranci.

By ukarofi