Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da karatu na biyu na ƙudirin da ke neman soke Dokar Zaɓe ta 2022 domin samar da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2025.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar yayin zaman majalisa a ranar Laraba bayan mafi yawan ‘yan majalisa sun goyi bayan ƙudirin ta hanyar ƙuri’ar murya.
Bayan haka, an miƙa ƙudirin zuwa Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zaɓe domin ƙarin nazari da shirya sauraron jama’a. An umurci kwamitin da ya dawo da rahoto cikin makonni biyu.
ƙudirin, wanda Shugaban Kwamitin Zaɓe na Majalisar Dattawa, Sanata Simon Lalong (APC, Filato ta Kudu) ya gabatar, na da nufin ƙarfafa tsarin doka da ke jagorantar gudanar da zaɓe a Nijeriya.
An fara gabatar da ƙudirin ne don karatu na biyu a makon da ya gabata, amma aka dage don samun ƙarin shawarwari. Sai dai an sake komawa kai a zaman Laraba, inda ‘yan majalisa suka tattauna a kan muhimman ƙa’idojinsa.
Dalilan gyaran dokar
Yayin da yake gabatar da ƙudirin, Sanata Lalong ya yaba wa Dokar Zaɓe ta 2022 saboda sabbin gyare-gyaren da ta kawo, amma akwai wasu matsaloli da ya lissafi kamar haka:
Jinkiri wajen sakin kuɗaɗen zaɓe, rikice-rikice kan rajistar masu zaɓe, saɓani kan yadda ake tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura, da kuma rashin sahihan damammaki da zai gaggauta hukunta masu aikata laifukan zaɓe.
Ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta ƙara tabbatar da ’yancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta hanyar kare ta daga tsoma bakin siyasa da ikon gwamnati.
Muhawara a Majalisa
A yayin tattaunawa, Sanata Adamu Aliero (APC, Kebbi ta Arewa) ya nemi a ƙara tanadi kan tura sakamakon zaɓe ta na’ura.
Ya kuma buƙaci a ƙarfafa amfani da na’urar BVAS don tabbatar da gaskiya da bayyananniyar hanya a zaɓe.
Sanata Orji Kalu (APC, Abia ta Arewa) ya shawarci ’yan majalisa, ciki har da ’yan adawa, da su haɗa kai wajen gina tsarin zaɓe mai gaskiya da amana.
Sanata Tahir Munguno (APC, Borno ta Arewa) ya nemi gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu cikin gaskiya, rage kuɗaɗen zaɓe, da ƙarfafa matakai kan sayen ƙuri’a.
Sanata Agom Jarigbe (PDP, Cross River ta Arewa) ya goyi bayan amfani da tura sakamakon zaɓe ta na’ura da kuma ba da dama ga ’yan takara masu zaman kansu.
Sanata Olalere Oyewunmi (PDP, Osun ta Yamma) ya bukaci hukunci mai tsauri ga masu aikata laifukan zaɓe, ciki har da jami’an INEC da na tsaro da ke lalata zaɓe.
Oyewunmi, wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye, ya koka cewa yawancin masu laifin zaɓe ba sa samun hukunci mai tsanani.
Sanata Patrick Ndubueze (APC, Imo ta Arewa) ya bayar da shawarar cewa a tattara sakamakon zaɓe kuma a sanar da shi cikin awanni shida bayan kammala ƙuri’a.
Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo ta Arewa) ya bukaci a kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a zaɓe, yana zargin wasu ’yan siyasa da daukar ’yan daba don tada rikici.
Sanata Seriake Dickson (PDP, Bayelsa ta Yamma) ya ba da shawarar a bai wa INEC cikakken iko wajen tantance wanda ya ci zaɓe da kuma hana jam’iyyun siyasa yin amfani da iko fiye da kima.
Jawabin Shugaban Majalisa
A cikin jawabin rufewa, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sahihancin zaɓe a Nijeriya ya inganta tun bayan da jam’iyyar APC ta karɓi mulki a 2015, amma akwai bukatar ƙarin gyare-gyare don samun cikakkiyar gaskiya.
Muhimman Abubuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2025 Ya Kunsa
Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2025 ta ƙunshi gyare-gyare da nufin ƙarfafa tsarin gudanar da zaɓe a Nijeriya, tabbatar da ’yancin INEC, da ƙara gaskiya da amana a harkokin siyasa da zaɓe.
Muhimman sassa sun haɗa da:
Sashe na 3(3): Ya wajabta sakin kuɗaɗen INEC da wuri domin shirye-shiryen zaɓe su gudana cikin lokaci.
Sashe na 5: INEC za ta rika gabatar da bayanan kuɗinta da aka duba cikin watanni shida bayan ƙarshen kowace shekara ta kuɗi.
Sashe na 10(2)(c): Ya ƙara Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) a matsayin sharadi wajen yin rajistar masu zaɓe.
Sashe na 12(1)(d) da 12(2): Sun amince da damar fursunoni (masu zaman gidan yari) su yi rajista da kada ƙuri’a idan INEC ta shirya musu dama.
Sashe na 27(5–7): Ya tsara jadawalin zaɓe da ya wajabta a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni aƙalla kwanaki 185 kafin ƙarshen wa’adin mai ci.
Sashe na 44: Ya gabatar da tanadi soma zaɓe da wuri kafin ranar zaɓe da aka saka na gama gari (early voting).
Sashe na 60(5): Ya wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura don ƙara gaskiya da rage maguɗi.
