Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dangantakarsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tana nan daram ba tare da wata matsala ba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano ranar Laraba.
Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron bikin cika shekaru 69 na haihuwar Sanata Kwankwaso wanda aka gudanar a ƙaramar Hukumar Madobi, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan zagayowar ranar haihuwarsa.
Gwamnan ya sake jaddada cikakken goyon bayansa ga ci gaba da raya manufar tafiyar Kwankwasiyya, wacce ke taka muhimmiyar rawa wajen cigaban jihar Kano.
“Ina tabbatar wa mabiyan tafiyar Kwankwasiyya cewa za mu ci gaba da bin tsarin akidarta, kuma muna aiwatar da sabbin shirye-shirye don tabbatar da hakan,” in ji Yusuf.
Ya kara da cewa duk wanda ke sa ran rabuwar kai a cikin tafiyar Kwankwasiyya zai gamu da baƙin ciki, domin tarihin rayuwar Sanata Kwankwaso tun daga ƙuruciya har zuwa shugabanci ya kasance abin koyi.
Yusuf ya gode wa Farfesa Kamilu Fagge da Farfesa Bello Kano bisa addu’o’in da suke yi domin Allah ya kare jihar daga masu neman tayar da hankula a lokacin mulkinsa.
A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya yaba da irin ci gaban da ake samu a karkashin gwamnatin Yusuf, tare da godiya ga dimbin jama’ar da suka fito daga Kano da sauran wurare domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
