Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An shawarci Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa a shirin da take na sake yin auren gata na mutum 2,000, ta yi amfani da iyayen ƙasa, hakimai, dagatai da masu unguwanni a tafi cikin unguwanni da ƙauyuka a duba su wanene auren ya ƙi yiwuwa saboda rashin kayan ɗaki, wace ce auren ya ƙi yiwuwa saboda rashin katifa ko wani muhimmin abu a zaƙulo irin waɗannan mutanen gwamnati ta yi tanadin da ya kamata a taimaka musu a yi auren.
Bashir Isma’ila Kabawa, Babban Darakta na Gidauniyar “Save Life Sustainable and Counseling Initiative” Gidauniyar inganta rayuwa da bayar da shawarwari daga tushe ne ya bayar da shawarar da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce auren da aka yi zuwa ake a nemo, mutane da a cikinsu wasu ma da dama suna da halin da za su yi, a ba su kayan ɗaki da jari da kayan abinci a ce an yi auren, amma ba cewa yake abin da ake ba shi da kyau ba, shawara ce dai yake ganin wannan hanyar ya kamata a bi ta amfani da iyayen ƙasa a zaluƙo yara marayu da masu iyayen da ba su da hali abi hanyar da duk ya kamata a bi a yi auren.
Babban Darakta na Gidauniyar ta inganta rayuwa da bada shawarwari daga tushe, Bashir Isma’ila Kabawa ya ƙara da yin kira da cewa ko a mutane da suke taimakawa masu larurar HIV akwai mataki da ya kamata abi na sirri domin suma su riƙa amfanar da auren da Gwamnatin Kano take, don ba za yiwu kana da larurar ka zo ka ce kana da ita ba.
Ya ce akwai hanyoyi da ya kamata gwamnati ta bi da za a shigo da waɗannan bayin Allah abu ne da ba za a gayawa duniya shi ba, amma dai in gwamnatin ta buƙaci hakan akwai hanyoyin da ya kamata su faɗa da za a shigo da masu larurar HIV saboda suma suna da buƙata sosai da a yanzu ma za su iya kawo mutum 50 a ɓangarensu.
Bashir Isma’ila ya ce sun kafa gidauniyar ne saboda mutane masu larura mai karya garkuwar jiki don kore musu tsangwama kuma su ba su taimako da za su iya ba su akan waɗannan.
Ya ce abinda ya jawo hankalin su akwai wani da suke tare da shi ɗan unguwar makafin Dala tsawon shekaru yana gwagwarmaya a cikin waɗannan bayin Allah yau da gobe in za a yi taro yana kiransa su tafi sai ya kalli irin fama da tsangwama da kyama da ake musu a cikin al’umma don haka ya ga dacewar ya dawo inda yake don samar da wannan ƙungiya domin suna da irin waɗannan mutane a cikin al’umma don a riƙa taimaka musu.
Ya ce shekaru huɗu kenan da yi wa gidauniyar rijista sun soma ayyuka ne daga matakin ƙaramar hukumar Dala har ta bunƙssa ta zama ta matakin jihar Kano har ma da wasu jihohi suna aikin tallafawa bayin Allah suna kuma samun nasarori suna haɗa aurratayya a tsakanin masu larurar.
A baya su suke zuwa su nemo su, amma an sami cigaba suna zaune wani zai zo tsakanin maza da mata yace yanada larurar a nemo masa ɗan’uwa mai larurar don su yi aure.
Ya yi nuni da cewa an samu cigaba sosai saɓanin da, don gudun kar a gane kana da larurar, mutum sai ya ɓoye kansa, kuma ba a damu da gwaji ba, mace za ta je ya auri wanda yake lafiya ko shi namiji ya auri mai lafiya azo a haɗu maimakon a rage yawan yaɗuwarta sai ya ƙaru, yanzu an sami cigaba yanda al’umma ke iya zuwa suce suna da larurar a haɗa su da mai irin larurar su aura a haka sun haɗa aure sama da 100.
Babban Darakta na Gidauniyar inganta rayuwa da bayar da shawarwari daga tushe ya ce daga ƙalubale da suke fuskanta shine da suna haɗa aure na masu ɗauke da larurar cutar mai karya garkuwa, amma yanzu wani yanayi yasa kowa da mai larurar da wanda bashi da ita suna zuwa neman aure kuma a matsayin su na masu haɗa aure suna fuskantar raini da yi musu wani kallo na rashin daraja wanda kuma wannan aiki ne da suke saboda Allah da kyakkyawar manufa ga al’umma.
