
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai je kotu a matsayin shaida a shari’ar Nnamdi Kanu ba, wato tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB) don kaɗai an zayyano sunansa a jarida.
Wike ya ce, idan kotu ta gayyace shi domin tabbatarwa ko bada hujja, to zai je ba tare da wani jinkiri ba.
Ministan ya bayyana haka ne a Abuja yayin tattaunawa da ƴan jarida, inda ya ce babu wanda ya buƙace shi da ya je kotu domin yi wa Kanu shaida.
Ya kuma ce, kasancewar sunansa ya fito a jarida ba shi ke nuna cewa ya zama tabbataccen shaida ba, saidai idan kotu ta gayyaci shi to zai je ya domin kare kansa bisa biyayya a gare ta.
Ya ƙara da cewa, kwata-kwata ba shi da masaniya akan Kanu ya sanya shi a matsayin ɗaya daga cikin shaidunsa, a cewarsa, akwai buƙatar a ji dalilin Shugaban IPOB ɗin akan yin hakan.
Ana tuhumar Kanu ne da laifin ayyukan ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya sanya sunan Wike a matsayin ɗaya daga cikin shaidun nasa.
Sauran waɗanda ya lissafo sun haɗa da tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya); tsohon Shugaban sojoji, Janar Tukur Buratai (mai ritaya); Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas; da Gwamna Hope Uzodinma na Imo.
Haka kuma, akwai Ministan Ayyuka, Dave Umahi, da tsohon gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu.
