Naɗa hakimai biyar da Hakimin gundumar Kunya ya yi zai kawo cigaba — Jarman Kunya

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Daya daga cikin hakimai biyar da mai girma Hakimin Gundumar Kunya, Alhaji Ali Ado Bayero, ya naɗa, zai kawo gagarumin cigaba da ƙarfafa haɗin kan al’ummar Kunya da Minjibir, kamar yadda Jarman Kunya, Alhaji Sunusi Adamu Sa’ad Kunya, ya bayyana bayan naɗin da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce wannan amana da aka ɗora musu ba za su yi watsi da ita ba, kuma za su ci gaba da taimakawa jama’a a kowane fanni domin cigaban al’umma.

Shi kuwa Farfesa Sani Malumfashi, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano (KANSEIC), ya bayyana cewa wannan naɗa zai kawo cigaba a zamantakewa da sauran fannoni na rayuwar ɗan Adam.

Hajiya Ummi Aminu ta bayyana cewa naɗin Jarman Kunya da sauran hakimai abu ne na farin ciki da cigaba, tana addu’ar alkhairi ga hakimin Kunya da masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu.

A ƙarshe, Ambasada zaman lafiya, Alhaji Maldini, ya bayyana cewa Chiroman Kunya mutum ne mai sauƙin kai da son taimakon jama’a, kuma za a samu cigaba sosai da kasancewarsa cikin sabbin hakimai biyar.

By ukarofi