Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Ƙungiyar haɗin kan Funtua ƙarƙashin shugaban ta kwamred Mannir Suleiman ta yi wannan kira a wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar.
Ya ce ya kamata ƙaramar hukumar ta dawo da shirin tsabtace muhalli da ada ake gudanarwa a kowane karshen wata kamar yadda wasu ƙananan hukumomin Katsina ke gudanarwa.
Kwamred Suleiman ya ce dawo da shirin tsabtace muhalli a ƙaramar hukumar zai taimaka wajan rage cututtuka masu yaɗuwa a yankin musamman a garin Funtua.
Haka kuma idan ana tsabtace muhalli a duk wata zai kawai da cutar Maleria da ya zama ruwan dare sakamakon cizon sauro.
Shugaban ƙungiyar wanda kuma tsohon malamin kiwon lafiya ne ya bayyana cewa Ƙungiyar shi da duka sauran ya’yan ta, za su shiga aikin tsabtace muhalli a duk lokacin da za a gudanar.
Sai yayi kira da shugaban ƙaramar hukumar Funtua da ya bi sahun takwarorin sa wadanda sun riga sunyi nisa da farfaɗo da shirin.
Haka kuma kwamred Mannir Suleiman ya shawarci shugaban ƙaramar hukumar da ya mai da aikin tsabtace ofisoshi da harabobi na ƙaramar hukumar ya zama doka a duk baya sati biyu.
Ya yaba wa gwamnatin jihar Katsina da karamar hukumar Funtua bisa ƙoƙarin da suke wajen inganta harkokin lafiya a jihar, musamman a yankin Funtua.
Shugaban ƙungiyar ya tabbatar da cewa mambobin ƙungiyar a shirye suke wajen bada ta su gudunmawa ba kan kiwon lafiya ba kaɗai har da duk wasu tsare tsare na da zai kawo cigaba a ƙaramar hukumar.
