Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da gasar al’adu da fasaha ta farko a tarihin jihar wacce aka sani da Kano Festival of Arts and Culture (KANFEST), wadda aka shirya domin nunawa duniya ɗaukaka da wadatar al’adu na Kano tare da ƙarfafa haɗin kai, ƙirƙira da ci gaban tattalin arziki.
An gudanar da bikin buɗewar ne cikin wani katafaren ɗakin taro mai kayatarwa da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin al’adu, masana fasaha da baƙi daga cikin Najeriya da kasashen waje.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Yusuf ya bayyana KANFEST a matsayin “babbar alama ta al’adu da sabon babi a tarihin Jihar Kano.
Ya tunatar da cewa tun tsawon ƙarni da dama, Kano ta kasance cibiyar kasuwanci, ilimi, sana’a da bunƙasar wayewa a nahiyar Afrika.
“Kano ta mallaki wani muhimmin tarihi da ya shafe sama da shekara dubu. Daga ramin tuka launin nan na Ƙofar Mata, zuwa masana’antar fata da ta shahara a duniya, kiɗa, tufafi, harshe da gine-ginenmu su ne alfaharin wayewar Bahaushe,” inji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa wannan biki ba wai nishaɗi kawai ba ne, har ma wata hanya ce ta ƙarfafa matasa, bunƙasa yawon bude ido, da haɓaka harkar ƙirƙire ƙirƙire.
“Al’ada ba tarihi kawai ba ce, al’ada tattalin arziki ce. Tana samar da ayyukan yi, tana buɗe kasuwanni, tana inganta ƙirƙira. A matsayinmu na gwamnati, mun ƙuduri aniyar tallafa wa masu fasaha da masu sana’o’i domin su haɓaka basirarsu da damar cigabansu.
Gwamna ya yi maraba da baƙi daga cikin gida da waje, inda ya bayyana Kano a matsayin gari mai kyakkyawar karɓa, zaman lafiya da himma ta kasuwanci, tare da kira ga jama’a da su ƙara haɗuwa da nuna kishin al’adu.
A yayin bikin, an gabatar da nune-nunenkayan gargajiya, ayyukan hannu, kiɗa, rawa, kayatattun tufafi, tatsuniya da sauran wasannin kwaikwayo.
An yi hasashen cewa KANFEST zai taimaka wurin faɗaɗa yawon buɗe ido, jawo jarin ɗan kasuwa, da ƙara matsayi da martabar Kano a matsayin babban cibiyar al’adu a Najeriya da Afrika ta Yamma.
Da yake rufe jawabin nasa yayin ƙaddamar da KANFEST, Gwamnan ya tabbatar da cewa za a riƙa gudanar da bikin a duk shekara domin ya ci gaban kawo tasiri ga tattalin arzikin Kano.
Da yake jawabi a yayin taron mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya jaddada rawar Kano a matsayin cibiyar wayewa, kasuwanci da ilimi tun tarihi.
“Wannan biki ba nishaɗi kaɗai ba ne, tunatarwa ne game da asalinmu mu al’umma ce mai mutunci da al’ada. Dole ne mu kiyaye tarihi mu isar da shi ga waɗanda ke zuwa bayanmu.”
Ya yi kira ga matasa da su riƙe addini, ladabi, aiki tuƙuru, da kishin al’umma.

Shima a nashi jawabi Jakadan Rwanda a Najeriya, Mista Christopher Bazivamo, ya yaba wa Kano bisa farfaɗo da al’adunta, yana mai cewa al’adu tushen ci gaban al’ummar duniya ne.
Ya bayyana cewa darussa daga gina ƙasar Rwanda bayan faruwar rikicin 1994 sun dogara ne akan haɗin kai, dogaro da kai da darajar asalin al’umma.
Ya kuma sanar da cewa Rwanda yanzu tana ba duk ‘yan Najeriya da ‘yan Afrika damar shigowa ƙasar ba tare da visa ba, domin ƙarfafa yawon bude ido da musayar al’adu.
“Rwanda na nan tana son ƙarfafa hulɗar kasuwanci, yawon buɗe ido da al’adu da Najeriya, musamman Jihar Kano. Afrika za ta yi ƙarfi ne idan muka tashi tare.
