Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Qatar Charity wata ƙungiya ce taa jin ƙai mai zaman kanta a kasar Qatar da ke zaune a Najeriya,ta yi alƙawarin samar da sabbin kayan aikin likitanci ga asibitocin Katsina da cibiyoyin lafiya matakin farko (PHCs).
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin da ke taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma, musamman mata, yara, matasa, da kuma marasa galihu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Qatar Charity Nijeriya, wata yarjejeniya da za ta buɗe sabon babi na haɗin kai a fannin ayyukan jin kai da ci gaban zamantakewa a faɗin jihar.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana wannan yarjejeniya a matsayin tsari na haɗin gwiwa da tuni yake da sakamako ta fannin ƙarfafa sana’o’i, kiwon lafiya, da ilimi. “Muna matuƙar godiya da goyon bayan ku,” in ji Gwamnan.
“Taimakon ku ya taimaka sosai wajen inganta rayuwar jama’ar mu. Kwanan nan ma kun zo kun raba kayan tallafi, kuma wannan ya kawo sauƙi ga iyalai da dama a faɗin jihar.”
Ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta ƙarfafa dangantaka mai ɗorewa tsakanin ɓangarorin biyu. “Wannan yarjejeniya ta kafa tsarin alhakin juna. A matsayina na gwamnati, za mu cika alƙawuranmu kuma mu tabbatar da ɗorewar dukkan ayyukan Qatar Charity a Katsina,” in ji shi.
Gwamnan ya yaba wa Qatar Charity bisa sadaukarwa da taimakon da ta ke yi tun kafin wannan yarjejeniya. “Tun kafin wannan abin alheri ,Qatar Charity ta yi abubuwa da dama a Katsina State. Muna godiya ƙwarai da irin wannan taimako mai ɗorewa,” ya ƙara da cewa.
Raɗɗa ya kuma roƙi ƙarin tallafi a fannin ilimi. “Muna son ganin irin manyan cibiyoyin ilimi masu fa’ida da kuka gina a wasu jihohi a nan Katsina. Mutanenmu sun cancanci irin waɗannan ayyuka, kuma za ku iya dogaro da mu a matsayin aminan haɗin gwiwa,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da yarjejeniyar cikin gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa tana daidai da shirin sa na “Building Your Future” wanda ya mayar da hankali kan bunƙasa jari-hujja ta bil’adama.
“Manufarmu ita ce ƙarfafa cibiyoyi da suke da tasiri kai tsaye a rayuwar jama’a kamar makarantu, asibitoci, da cibiyoyin tallafi. Haɗin gwiwa irin wannan yana taimaka mana cimma waɗannan manufofi cikin sauri,” in ji Gwamnan.
A nasa jawabin, daraktan ƙasa na Qatar Charity a Najeriya, Mista Assem Abu Al Shaer, ya tabbatar da goyon bayan ƙungiyarsa ga hangen nesan Gwamna Raɗɗa ta hanyar aikace-aikacen da ke tasiri kai tsaye ga al’umma.
Mista Al Shaer ya yaba da jagorancin Gwamnan mai daidaita kai da gaskiya, yana mai cewa irin waɗannan ɗabi’u ne ke jawo hankalin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu sahihanci zuwa jihar.
A ƙarƙashin sabon yarjejeniya, Qatar Charity ta sanar da cewa za ta bayar da ƙarin kayan aikin likitanci don inganta harkar kiwon lafiya. A ƙarƙashin wannan shiri, duk sabbin cibiyoyin lafiya da aka gyara za su samu na’urorin Electronic Blood Pressure Machines, yayin da manyan asibitoci 15 za su samu kujerun guragu na lantarki (Electric Wheelchairs) domin taimaka wa marasa lafiya masu buƙata ta musamman.
Mista Al Shaer ya bayyana cewa wannan tallafi yana cikin manufar Qatar Charity ta duniya wadda ke nufin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da kuma samar da damar kula ga marasa galihu.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da haɗin kai da Gwamnatin Jihar Katsina a fannoni na kiwon lafiya, ilimi, da ƙarfafa tattalin arziki.
Yarjejeniyar ta fayyace rawar da kowanne ɓangare zai taka. Qatar Charity, ƙungiya ce ta ƙasa da ƙasa da aka yi rijista bisa doka a Najeriya, ita ce ɓangare na farko, yayin da Gwamnatin Jihar Katsina ita ce ɓangare na biyu wadda ta ɗauki nauyin aiwatar da manufofi masu inganta walwalar jama’a.
Yarjejeniyar ta ƙunshi manyan fannoni da suka haɗa da: Ilimi (gina makarantu, tallafin karatu, da kayan koyo), Kiwon lafiya (aikin jinya, tiyata, da sabunta asibitoci), gidaje na jin ƙai, Shirye-shiryen ƙarfafa sana’a (kayan ɗinki, babura, da kayan gona), Samar da ruwa, abinci, da taimakon gaggawa.
A wajen bikin sanya hannu, mai ba da shawara ta musamman kan ilimin ’Ya’ya Mata, Hon. Jamila Abdu Mani, wadda ta jagoranci shirya yarjejeniyar ta bayyana farin cikinta da wannan cigaba. “Wannan haɗin gwiwa zai buɗe sababbin damar cigaba ga mata da ’ya’ya mata,” in ji ta.
“Muna alfahari da rawar da muka taka wajen samar da wannan haɗin kai, kuma muna sa ran sakamako mai kyau a fannin ilimi, lafiya, da jin daɗin jama’a.”
Haɗin gwiwar ya samo asali ne daga gyare-gyaren da Gwamna Raɗɗa ke ci gaba da yi a fannin lafiya, ciki har da sabunta asibitoci, samar da kayan aiki, da ɗaukar ma’aikatan lafiya musamman a yankunan karkara.
Da wannan sabon tallafin daga Qatar Charity, ana sa ran samun gagarumin ci gaba wajen samun kulawar lafiya a matakin farko da na biyu, musamman a cikin al’umma masu ƙarancin albarkatu.
Gwamnatin Raɗɗa ta ci gaba da samun amincewar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu sahihanci saboda gaskiya da shugabanci mai mayar da hankali kan jama’a. Wannan haɗin kai ya ƙara jaddada cigaban da ake samu a fannoni na ilimi, lafiya, da ci gaban zamantakewa a Katsina.“Wannan yarjejeniya alama ce ta bege da jin ƙai,” in ji Gwamna Raɗɗa.
“Tare, muna nuna cewa tausayi idan aka mayar da shi tsari ta hanyar haɗin kai, yana iya sauya rayuka da gina kyakkyawar makoma.”
