Gwamnan Kano umarci sarakuna su cigaba da bukujuwan hawan daba na shekara-shekara

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan Umarnin Gudanarwa (Executive Order) da ya buƙaci dukkanin masarautun gargajiya na Kano, Rano, Gaya, da Karaye su ci gaba da shirya bikin hawan daba na shekara-shekara (Durbar Festival) duk da takunkumin da hukumomin tsaro ke ta maimaitawa a kwanakin baya.

An sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da bikin farko na Kano Festival of Arts and Culture (KanFest), wanda ake kira “Kalankuwa”

Kalankuwa wani shiri da aka ƙirƙiro don farfaɗo da al’adun Kano da kuma yaɗa su ga duniya.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa bikin hawan Sallah wanda ke ɗauke da fitar jaruman dawakai, kayan ado na gargajiya, da nuna girman masarauta, ya samu karɓuwa a duniya tun bayan UNESCO ta saka shi cikin jerin muhimmiyar gadon al’ada na duniya da bai kamata ya shuɗe ba.

UNESCO ta yaba da bikin ne saboda muhimmancinsa wajen tarihi, fasaha, da kuma yadda yake ƙarfafa haɗin kai da biyayya a cikin tsarin masarauta.

“UNESCO ta gano cewa bikin hawan Sallah ya sanya Kano cikin fitattun wuraren al’adu na duniya, kuma ya tabbatar da rawar da al’adunmu ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da martaba,” in ji Gwamna Yusuf.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tare da dukkan ƙananan hukumomi 44 za su ci gaba da tallafawa masarautu don tabbatar da ɗorewar wannan abin da ya kira “gado abin girmamawa daga kakanninmu.”

Yusuf ya jaddada cewa kare al’adu ba kawai jin daɗi ba ne, amma muhimmin ɓangare ne na tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatinsa.

“Al’ada ba abin tarihi ba ce kawai, wata kafa ce ta ci gaba ga ƴa’ƴanmu na gaba,” in ji shi. “Farfaɗo da al’adu da yawon buɗe ido na daga cikin shirye-shiryenmu don samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki, da ƙarfafa zumunci tsakanin al’umma.”

Gwamnan ya bayyana Kano a matsayin gari mai tarihi wajen ilimi, kasuwanci, sana’o’i, ƙirƙira da wayewa, yana mai cewa alfaharin al’adu shi ne tushen ƙarfin juriya da ci gaban jihar.

Ya bayyana wasu muhimman matakai da gwamnati ke ɗauka don kare gadon al’adun Kano, ciki har da:

Gyaran cibiyar ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido.

Sabunta hukumar tarihi da al’adu zuwa cibiyar bincike ta zamani

Mayar da ginshiƙan tarihi a cikin birnin Kano.

Gina gidan Makama da ya rushe.

Sabunta Magwan (Leather Hub) don tallafa wa masu sana’ar fata.

Da kuma shirin dawo da katangar birnin Kano da ƙofofinta na tarihi da ake kwatanta su da “alamar haɗin kai, ƙarfi da wayewa.”

A nasa jawabin, mataimakin Gwamna, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana cewa KanFest an shirya shi ne domin nuna basirar ƴan Kano ta fannin fasaha, labarai, kide-kide, wasan gargajiya da kasuwancin ƙere-ƙere.

“Al’ada ba nishaɗi kaɗai ba ce, hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki da samar da zaman lafiya,” in ji Gwarzo.

A dai wannan biki, Jakadan Rwanda a Najeriya, Christophe Bazivamo, ya yaba wa jihar Kano bisa wannan shiri, yana mai cewa hakan na ƙarfafa ainihin al’adun Afirka.

“Da zarar muka koma ga asalinmu, to za mu gina haɗin kai da mutuncin al’ummarmu,” in ji shi.

Bikin na Kalankuwa ya samu halartar sarakuna da jakadu da jami’an gwamnati da ƴan kasuwa, da masoya al’adu daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.

By ukarofi