
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani sabon rikici na neman kunno kai a Babar jam’iyyar adawa ta PDP bayan da aka amince da naɗin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci, Tanimu Turaki (SAN) a matsayin ɗan takarar yarjejeniya na shugabancin jam’iyyar yayin tunkarar babban taronta da za a yi a 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo.
Zaɓin, wanda aka yi bayan zaman masu ruwa da tsaki na ƴan PDP na yankin arewa ƙarƙashin jagorancin gwamnoni da jiga-jigan ƴan jam’iyya, ya samu tsaiko ne a yayin da ɓangarorin tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo da tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike suka ƙi amince wa da shi.
Al’amarin ya buɗe mikin ɓarakar da ke tsakanin ƴaƴan jam’iyyar duba da ƙoƙarin gyara da take yi, wanda kuma ya haifar da sabon cecekuce kan raba manyan muƙamai da rashin daidaito akan haka.
Bayan zaman majalisar zartarwar jam’iyyar a watan Agusta a Abuja, PDP ta cimma matsayar bada tikitin takarar shugaban ƙasa ga shiyyar kudu, yayin da shugaban jam’iyya kuma zai zama daga arewa.
Akan haka ne aka zaɓo mutane uku daga Arewa ta Yamma waɗanda sune; Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna; Sule Lamido, tsohon gwamnan Jihar Jigawa; da kuma tsohon minista, Tanimu Turaki.
Saidai wannan hukunci bai yi wa magoya bayan Lamiɗo daɗi ba domin kuwa suna ganin an yi haka ne ba tare da faɗaɗa tuntuɓa ba da kuma ƙoƙarin nuna fifikon cancanta ga tsohon ministan.
Haka ma ƴan Wike, waɗanda suke goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, saboda sun fi yarda a bada shugabancin ga ɗan yankin Arewa ta Tsakiya a madadin ɗan ta Yamma.
