
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da bashin da suke bin Gwamnatin Tarayya ke cigaba da hauhawa, ƴan kwangilar raba abinci a gidajen gyaran hali sun koka tare da yin gargaɗi cewa hakan ka iya shafar aikin da haifar da barazanar tsaro.
Masu raba abincin sun ce, gwamnati ta riƙe musu jimillar kuɗin ciyarwa da adadinsa ya kai Naira biliyan 30 ciki har da biliyan N7.7 na ragowar kuɗin aikinsu na ƙarshen shekarar 2023 da kuma biliyan N23 na rashin aiwatar da ƙarin kuɗaɗen alawus ga fursunoni daga ɓangaren gwamnatin tarayyar.
A watan Agustan 2024 ne Fadar Shugaban Ƙasa ta amince da ƙarin kuɗin abincin kowane fursuna daga N750 zuwa 1,125 sakamakon hauhawar farashin kayan abinci, lamarin da aka yi tsammanin ya fara aiki a watan.
Saidai sama da shekara guda kenan, ƴan kwangilar sun ce har yanzu ana biyansu ne da tsohon tsarin na N750 ga kowane fursuna.
Hakan ya jefa da dama daga cikin ƴan kwangilar cikin takura ta fuskar kuɗi duba da yadda da dama daga cikinsu suka koma cin bashi a bankuna kafin sun aiwatar da ayyukansu.
Wani daga cikinsu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce al’amarin ya wuce a cigaba da jure masa kasancewar yanzu haka ba a biya su ba na tsawon watanni kuma a haka ake buƙatar su cigaba da ciyar da dubunnan ƴan kurkuku.
