
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Laraba aka cire sunan matar nan da aka yanke wa hukunci bayan samun ta da laifin halaka mijinta, wato Maryam Sanda daga sahun waɗanda suka samu yafiyar shugaban ƙasa, bayan da Shugaba Bola Tinubu ya amince da gyararren jaddawalin waɗanda aka yi wa afuwa da aka miƙa da fari domin aiwatarwa.
Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa kisan mijinta Bilyaminu Bello, an sanya sunanta ne acikin waɗanda aka yafewa da fari, lamarin da ya haddasa cecekuce acikin al’umma.
Saidai, cire ta da aka yi a yanzu ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta miƙa wuya ga matsin da ta samu daga ɓangaren al’umma da kuma al’amarin da ya shafi tsaro.
A cewar wata takarda daga Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya sanya hannu akan sharuɗɗan doka game da al’amarin, kamar yadda dokar ƙasa ta ba shi iko.
Onanuga ya bayyana cewa shawarwari da tuntuɓa daga ɓangaren majalisar tsofaffin shugabanni da hukumomin tsaro gami da cecekucen al’umma ne ya haifar da cire sunayen wasu daga cikin mutanen da aka yanke wa hukunci kan wasu laifuka.
Ya ƙara da cewa, sake nazari akan batun abu ne mai muhimmanci ga tsaron ƙasa, zimmar doka ga jami’an hukumomin tsaro da adalci ga waɗanda lamarin ya shafa kai-tsaye da kuma ɗaukacin al’umma.


