Kwamitin wayar da kai kan rajistar katin zaɓe a Kano ya ƙara faɗaɗa yunƙurinsa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kwamitin Wayar da Kai kan Rijistar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC), ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gudanar da muhimmin taron dabarun aiki domin nazarin ci gaban da aka samu tare da tsara sabbin hanyoyin ƙarfafa wayar da kan jama’a game da muhimmancin mallakar katin zaɓe.

Da yake jawabi bayan kammala taron, Kwamared Waiya ya bayyana gamsuwa da irin ci gaban da aka samu a jihar, inda ya ce Jihar Kano ta samu ƙarin matsayi a jerin jihohin da suka fi yawan masu rijista a faɗin ƙasa.

Kwamared Waiya ya danganta wannan nasara da haɗin kai tsakanin mambobin kwamitin, jajircewar abokan hulɗa da kafafen yaɗa labarai, da kuma karuwar fahimtar jama’a kan muhimmancin yin rajista.

Kwamishinan ya ƙara tabbatar da cewa, karkashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, gwamnati na da cikakken ƙudiri na ganin cewa kowane ɗan kasa mai cancanta ya samu damar yin rajista da kuma taka muhimmiyar rawa a tsarin dimokuraɗiyya.

Haka kuma ya gode wa dukkan kungiyoyi da abokan hulɗa da suka nuna goyon baya ga aikin kwamitin, tare da kiran sauran ƙungiyoyi, al’ummomi, da mutane masu kishin ƙasa da su shiga wannan yunƙuri.

“Za mu ci gaba da wannan azama don ƙarfafa halartar jama’a a harkokin dimokuradiyya da kuma tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyyarmu a Jihar Kano,” inji Waiya.

By ukarofi