A cikin shekara ɗaya mun gudanar da ayyuka 68 -Hon. Abba Utai

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Wudil, Hon. Abba Muhammad Tukur Utai, ya bayyana cewa a cikin shekara ɗaya kacal da ya shafe a ofis, ya samu damar aiwatar da aƙalla ayyuka guda 68 da suka shafi raya ƙasa da inganta rayuwar al’ummar yankin.

Hon. Utai ya bayyana hakan ne bayan zagayen gaishe-gaishe, duba marasa lafiya, da kuma ziyartar wasu daga cikin ayyukan da aka kammala a cikin shekara ɗaya da ta gabata, inda ya jaddada cewa nasarorin da aka samu sun kasance ne sakamakon sahalewar gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da haɗin kan majalisar ƙaramar hukumar, masu ba shi shawara, da kuma ma’aikata gaba ɗaya.

A cewarsa, “Mun aiwatar da ayyuka da dama musamman a bangaren ilimi, inda muka gyara makarantu, muka gina sabbin ajujuwa, muka kafa Islamiyyu da kuma masallatai a mazabu daban-daban. Mun ɗauki nauyin ɗalibai fiye da 500 ‘yan asalin karamar hukumar domin yin digiri a Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, da kuma wasu da aka tura kwalejoji domin karatun Difloma da NCE.”

Hon. Utai ya ƙara da cewa a bangaren lafiya, sun gudanar da ayyuka irin su samar da dakunan shan magani, gudanar da aikin ido da aikin ƙafa kyauta ga marasa galihu. Haka kuma, a bangaren sufuri, ya ce sun gyara hanyoyi da dama domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a a yankin.

“Rayuwa ba ta yiwuwa ba tare da ruwa ba, shi yasa muka samar da famfunan tuka-tuka, rijiyoyi da na’urar famfo mai aiki da hasken rana a dukkan mazabu goma da ke cikin karamar hukumar,” inji shi. 

Ya ƙara da cewa sun kuma tallafawa matan aure da gadaje da katifu domin inganta rayuwarsu.

Shugaban ya bayyana cewa al’ummar Wudil za su ci gaba da ganin sabbin ayyukan ci gaba a wannan sabuwar shekara, tare da yaba wa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa irin tallafi da goyon bayan da yake basu domin gudanar da ayyuka cikin nasara.

A nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar NNPP na yankin, Hon. Aminu Muhammad, ya bayyana cewa shekara ɗaya ta mulkin Hon. Utai ta fi shekaru takwas na baya wajen samar da ayyuka masu amfani ga al’umma. A cewarsa, “Zuwan sabon shugaban ya canza fuskar Wudil, inda yanzu garin ke zama abin koyi a fannin ci gaba da raya ƙasa.”

Shi ma shugaban sashen ilimi na karamar hukumar, Hon. Idris Ibrahim Indabo, ya yaba da namijin ƙoƙarin da ake yi a fannin ilimi, inda ya bayyana cewa duk wata matsala da ta addabi makarantun yankin yanzu an magance ta. Ya buƙaci a samar da motocin hawa da babura domin ma’aikatan da ke zagayen makarantu.

A ƙarshe, kungiyar Mila Road Kwankwasiyya, Wudil ta karrama Hon. Abba Muhammad Tukur Utai da lambar yabo bisa yadda ya sauya fuskantar garin Wudil ta hanyar gudanar da ayyukan ci gaba masu ma’ana.

By ukarofi