GCTC ta yaba wa SSA Bala ƙalarawi kan horar da matasa 130

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban cibiyar horar da matasa kan sana’o’in gargajiya da na zamani, Malam Mukhtar Musa ‘Yankaba, ya yaba wa mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa, Hon. Abbas Tijjani Bala Kalarawi, bisa daukar nauyin matasa 130 a fannin sana’ar kiwon kaji, kwamfuta, da harkokin sadarwa na zamani ta kafafen social media.

Mukhtar Musa ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da shirin horas da matasan da suka fito daga ƙananan hukumomin Nasarawa, Fagge, da Tarauni, ƙarƙashin cibiyar Global Concept Training Center (GCTC).

A nasa jawabin, Hon. Bala Kalarawi ya ce wannan aiki somin-tabi ne daga cikin irin taimakon da yake yi wa al’umma, kuma ya fito daga aljihunsa kai tsaye, ba tare da wata tallafi ba. Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da yake daukar nauyin matasa ba, domin hakan ya zama ɗabi’arsa tun daga gida.

Ya ƙara da cewa burin Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne ci gaban matasa da sauran al’umma. A cewarsa, irin wadannan shirye-shirye na horaswa za su ci gaba da gudana don gina matasa masu ilimi da sana’a a faɗin jihar.

By ukarofi