Boma-bomai da alburusai ba su san addini ba, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ce ƙalubalen tsaro a Nijeriya na buƙatar aiki kafaɗa-da-kafaɗa, inda ya bayyana hare-haren ta’addanci a matsayin abinda ke shafar kowane addini, ƙabila ko yanki.

Ya ce, yayin da aka yi amfani da makami wajen haddasa tsaiko ga zaman lafiya daga ƴan ta’adda, hakan ba ya bambancewa tsakanin mutane da manoma da sauran al’umma.

Ya bayyana cewa, gwamnatin yanzu ta riski matsalolin tsaro da dama a lokacin da hau karagar mulki, lamarin da ya sa ta ɗauki matakan daƙile ayyukan ta’addanci da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a sassan da ake fama da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

Shettima, wanda Mataimakin Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Haɗejia ya wakilce shi a taron masu ruwa da tsaki kan ci-gaban shiyyoyi da Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa ta shirya a Abuja ranar Alhamis, ya ce “Kowane mutum ko ofis da ke da hannu a shugabanci wajibi ne ya taka rawa a wannan muhimmin aiki na dawo da zaman lafiya a ƙasa.”

“Alburushi ko bom bai san yare ko addini ba. Idan maƙiya suka harbo shi yayin da mu ke zaune lafiya, ba ya bambancewa. Zai kashe manomi da ɗan kasuwa, sannan ya tarwatsa yankunanmu masu yaruka da addinai daban-daban”, inji Shettima.

Ya bayyana cewa, ba iya faɗa da ƴan ta’adda wajen magance wadannan matsalolin ba ne kaɗai, har da ƙoƙarin daƙile tunanin da ake ruɗar al’umma da shi wajen raba kawunansu.

Kazalika, mataimakin shugaban ƙasar ya kuma kirayi jagorori da su riƙa ƙoƙarin daƙile ire-iren matsalar da ke ƙarfafa rarrabuwar kai da tabbatar da isar da saƙonnin da za su riƙa janyo ra’ayoyin mabiya addinai da ƙabilu akan haɗin kai.

By Babaji