Yadda ake rufa-riufa kan matsalar tsaro a Kebbi – Rahoto

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Duk da irin zagin da ake yi na rufa-rufa da Gwamnatin Jihar Kebbi ke yi dangane da matsalar tsaro, bincike ya nuna cewa, gaskiyar magana a kullum sai ƙara bayyana ta ke yi. Wani bincike da Wakilin Blueprint Manhaja ya gudanar a waɗansu sassa daga Jihar Kebbi ya nuna a ƙaramar Hukumar Arewa ya nuna cewa, daga cikin makarantu 198 da suke akwai yanzu, aƙalla 144 sun koma kango, saboda babu ɗalibai ballantana malamai, domin kowa ya watse, saboda ’yan bindiga da Lakurawa sun mamaye yankin.

Waɗansu sahihan majiyoyi sun tabbatar da cewa, malamai da ɗalibai sun ƙaurace wa makarantun, saboda kauce wa shiga hatsarin ’yan bindiga, yayin da waɗansu mutanen sun gudu daga garuruwan nasu zuwa manyan garuruwan da suke kusa da su, kamar Kangiwa, Yeldu, Bachaka, Bui, Sarka, Gumundai, Jantullu da dai sauransu.

Yanzu haka dukkan uwayen ƙasar da suke ƙaramar Hukumar Arewa su kuma sun gudu tare da iyalansu, inda uwayen ƙasar Yeldu da Kangiwa da Jaffeji da Gumundai da Chibike da Gumundai suka yi hijira zuwa garin Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, inda su kuma uwayen ƙasar Bachaka da Lema da Jantullu da Sarka suka gudu zuwa garin Argungu, cibiyar masarautar daular Kabi, domin tsira da mutuncinsu da na iyalansu.

Wani matashi daga yankin na ƙaramar ƙukumar Arewa, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya bayyana cewa, su yanzu har ta kai ga sun zama jiki da mayaƙan Lakurawa, saboda akwai hulɗar kasuwanci tsakaninsu da su, sai dai inda matsalar ta ke ita ce, suna ɗora haraji akan dabbobinsu, amma idan suka biya harajin shikenan. Sai dai akwai waɗansu Fulani da suke shigar Lakurawa suna kawo musu hari suna kashe su suna wawashe dukiyoyinsu.

Waɗannan Lakurawa sukan sayi kayan abinci da sauran abubuwan amfani daga mutanen ƙauyukansu, musamman a ƙauyukan da suke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar a gundumomin Gumundai, Kangiwa, Jaffeji zuwa Bachaka.

Wakilin Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin ko da ɗaya daga cikin sarakunan, amma hakan ba ta samu ba, saboda sun nuna gwamnatin jihar ta saka musu takunkumi ga duk abin da ya shafi magana da ’yan jarida.

A baya-bayan nan, bayan Gwamna Malam Nasir Idris ya fito fili ƙarara yana ƙalubalantar cewa, babu sansanin ’yan ta’adda ko ɗaya a Jihar Kebbi, kuma idan da akwai shi, a zo a gaya masa, sai ga shi ’yan bindigar sun yi awon gaba da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Kebbi, Hon. Sama’ila Bamboo Bagudo, ɗan majalisa mai wakiltar yankin ƙaramar Hukumar Bagudo ta Gabas, wanda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton yana hannunsu, har ma an fitar da wani saƙon magana da aka ce an naɗa ne lokacin da ya ke magana da wani yaronsa yana ba shi umarnin a sayar da motocinsa a haɗa kuɗi a kai wa ’yan ta’addar, don ya sami kansa.

Dangane da kama wannan ɗan majalisar, al’ummar Jihar Kebbi sun yi ta tofa albarkacin bakinsu bisa zargin halin ko-oho da gwamnatin jihar ta yi, saboda kusan sati ɗaya da kama shi, amma Gwamna Nasir Idris yana can cikin duniyar Turai, maimakon ya katse wannan yawon da ya ke yi ya dawo gida, saboda ko ba komai wannan mutum shine mutum na huɗu a matsayi a jihar.

Wani ɗan asalin garin Bena, Malam Mujahid Abubakar Bena, a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, waɗansu ’yan siyasa da karnukan farautarsu na gwamanti da ba su kishin al’umma, suna ta yaɗa maganganun ƙarya dangane da harkar tsaro, inda suke cewa, gwamnatin Malam Nasir Idris ta kori duk ’yan ta’adda da ke yankin jihar, wanda waɗannan kalaman ba su yi wa ’ya’yan Masarautar Zuru daɗi ba, musamman mutanen yankin Bena inda a nan ne abin ya fi ƙamari, saboda a kullum sai an kawo hari a ɗaya daga cikin ƙauyukansu a kashe na kashewa a ɗauki na ɗauka, ba dare ba rana.

Ya kuma koka da zaɓaɓɓun ’yan siyasa da ke wakiltar yankunansu bisa ga rashin gaya wa gwamnatin jihar gaskiyar abin da ke faruwa a yankunansu, saboda duk sun kwashe iyalansu zuwa Birnin Kebbi.

A ɗaya ɓangaren kuma talakawa duk da ya ke sun nuna alhininsu bisa ga kama Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Kebbi da ’yan bindiga suka yi suna bayyana cewa, da manyan jami’an gwamnati ne ko ’ya’yansu waɗannan ’yan ta’addar ke ɗauka, da wataƙila talakawa za su rage wani raɗaɗi, saboda ga talauci ga yunwa ga kuma rashin zama lafiya, uwa-uba kuma an hana su noma.

A ɓangaren hukumomin tsaro dai kuma, ita ma Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kebbi a ƙarƙashin jagorancin Bello M. Sani ta ce, ta baza kamarta a cikin wani aikin haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro, don ceto babban ɗan siyasar.

By ukarofi