Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni daga Babban Birnin Tarayya Abuja sun nuna cewa wasu gidajen mai sun rage farashin litar man fetur, bayan da farashin shigo da mai daga ƙasashen waje ya sauka ƙasa warwas da farashin dillalan matatar Dangote.
An ruwaito cewa, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, wasu manyan dillalai kamar NIPCO, AA Rano, Eterna, da Empire Energy sun rage farashin su a sassa daban-daban na Abuja.
A cewar rahoton, NIPCO da AA Rano sun saukar da farashin su zuwa N940 a kan kowace lita, daga tsohon farashin N950 zuwa N955. Eterna na sayarwa kan N945, yayin da Empire Energy ke sayarwa N955, maimakon N959 da ake sayarwa a baya.
Wannan na nufin an sami ragin farashi daga N4 zuwa N10 kan kowace lita, dangane da gidan man da ake saya.
Haka kuma, NNPCL ya rage nata farashin daga N955 zuwa N945 a kowace lita. Sai dai wasu gidajen mai kamar MRS da Ranoil sun ci gaba da sayarwa kan N950 da N955 har zuwa safiyar Alhamis.
Wani manajan MRS da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “Wataƙila mu rage farashin mu daga baya, amma a halin yanzu muna sayarwa kan N950 a kowace lita.”
Rahoton ya ƙara da cewa, farashin shigo da lita ɗaya na man fetur ya faɗi zuwa N827.04 a ranar 3 ga Nuwamba, 2025, daga N829.77 da aka ruwaito a ƙarshen Oktoba.
Wannan na nuna cewa farashin dillalan Dangote ya fi na sauran tashoshin masu zaman kansu da kusan N2, yayin da farashin shigo da mai ya fi ƙasa da na Dangote da N44.96.
A baya, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince da kuɗin harajin shigo da mai da dizal na kashi 15, domin ƙarfafa tace mai a cikin gida da kuma tallafa wa matatar Dangote.
Sai dai masana a fannin makamashi sun ce wannan sabon haraji na iya haifar da ƙarin farashin man fetur idan ya fara aiki a makonni masu zuwa.
