Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata gungun matasa a ƙauyen Sokupkpan na ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun kashe babban limamin ƙauyen bayan sun zarge shi da haddasa mutuwar wani matashi ta hanyar tsafi.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka kashe, Mallam Abdullahi Audu, ya rasu ne a ranar Laraba bayan wasu fusatattun matasa sun yi masa dukan kawo wuƙa bisa zargin cewa shi ne ya haddasa mutuwar Ibrahim Gana, matashi mai shekara 25 da suka fito daga yanki ɗaya.
Lamarin ya tayar da hankula a cikin ƙauyen Sokupkpan, inda fargaba da ruɗani suka riƙa yaɗuwa tsakanin jama’a.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa kafin mutuwarsa, marigayi Gana yana fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba, kuma a lokuta da dama yana cewa limamin yana damunsa a mafarki.
A cewarsa, “Yana yawan cewa limamin ne ke haddasa masa ciwon da yake fama da shi. Da halinsa ya ƙara muni, sai wasu suka fara gaskata cewa mafarkansa gaskiya ne.”
Bayan rasuwar Gana, ‘yan uwansa – Mohammed Shaba, Mahmud Gana, da Ndakpotun Issa – sun tattara wasu matasa suka ɗunguma zuwa gidan limamin domin yin ramuwar gayya.
Duk da cewa dattawan yankin sun yi ƙoƙarin shawo kan lamarin, matasan sun ƙi sauraro, suka riƙa bugun limamin da sanduna da makamai har sai da ya mutu.
Wani ganau ya bayyana cewa, “Ba su saurari kowa ba. Suna ta ihu suna cewa limamin ya kashe Gana da sihiri.”
‘Yan sanda daga sashen Tsaragi sun isa wajen bayan faruwar lamarin, inda suka cafke mutane huɗu da ake zargi da hannu kai tsaye a cikin kisan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin “mummunan kisan da ba shi da hujjar shari’a.”
Ta ce, binciken farko ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga zato da imani marar tushe. “Mun kama mutum huɗu, kuma ana ci gaba da neman sauran da suka tsere.”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya la’anci kisan kuma ya gargadi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu. “Doka ce kawai za ta iya hukunta wanda ake zargi, ba tashin hankali ba,” inji ta.
An binne limamin da aka kashe bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da al’umma ke ci gaba da jimami da firgita bisa tashin hankalin da ya girgiza yankin.
