Majalisa ta umarci NAFDAC ta fara aiwatar da haramcin barasar leda daga Disambar 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayar da umarni ga Hukumar Kula da Abinci da Magunguna (NAFDAC) da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da cewa an aiwatar da haramcin haɗa barasa mai ƙarfi a kwalabe ko leda daga watan Disamba 2025, ba tare da wani ƙarin lokaci ba.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta ƙi amincewa da buƙatar wasu masana’antu na sake samun ƙarin shekara guda don ci gaba da samar da barasa a leda.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da Sanata Asuƙuo Ekpeyong ya gabatar, wanda ya buƙaci majalisar ta hana duk wani ƙarin lokaci ga matakin da aka daɗe ana shiryawa na daina haɗa barasa a leda.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin zaman majalisar, Sanata Ekpeyong ya tunatar da cewa NAFDAC ta ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masana’antu da hukumomin lafiya, domin bin ƙa’idar duniya wajen rage illolin shan giya mai sauƙin samu.

A shekara ta 2018, an rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Ma’aikatar Lafiya, Hukumar Kare Masu Amfani da Kaya (FCCPC), NAFDAC, da ƙungiyoyin masana’antu kamar AFBTE da DIBAN, domin a daina samar da irin wannan giya a hankali cikin shekaru biyar.

Manufar yarjejeniyar ita ce daƙile yaɗuwar giya tsakanin yara, matasa, direbobi, da sauran jama’a masu rauni, sakamakon sauƙin samun ta da arha.

Sai dai, duk da tsawon lokacin da aka bayar, gwamnatin tarayya ta sake bai wa masana’antu shekara guda ta ƙarshe a 2024 domin su kammala kayan da ke hannunsu kafin su koma tsarin marufi mai bin ƙa’ida — wato Disamba 2025 a matsayin wa’adin ƙarshe.

Sanata Ekpeyong ya nuna damuwa cewa wasu masana’antu na ƙoƙarin neman wani ƙarin lokaci, abin da a cewarsa zai iya rage tasirin ikon hukuma, cutar da lafiyar jama’a, da kuma kawo rashin daidaito tsakanin kamfanoni a kasuwa.

By ukarofi