Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawan Nijeriya ta gano gagarumin almundahana a harkar man fetur na ƙasa, inda ta bayyana cewa kusan Dala Biliyan 303 na iya ɓacewa daga cinikayyar man gida da ta ƙasashen waje.
Wannan bincike na musamman wanda Sanata Ned Nwoko ke jagoranta ya nuna cewa sakamakon binciken ƙwararru ya gano bambance-bambance da rashin daidaituwa a kuɗaɗen da suka kai kusan dala biliyan 22.
Binciken ya kuma gano giɓin dala biliyan 81 tsakanin bayanan da kamfanin NNPCL da Babban Bankin Nijeriya (CBN) suka bayar a shekarun 2016 da 2017 — abin da ya tayar da hankali a majalisar.
Haka kuma, rahoton ya ce fiye da dala biliyan 200 daga ribar man duniya ba a bayyana inda suka shiga ba tun daga 2015 zuwa yau, saboda rashin ingantaccen tsari da raunin sa ido daga hukumomin gwamnati.
Rahoton ya bayyana matsalolin da suka haɗa da rashin auna man da na’urorin da aka tabbatar da ingancinsu, rashin haɗin kai tsakanin hukumomi, da kuma gaza aiwatar da dokoki yadda ya kamata.
Kwamitin ya soki cire sashen Weights and Measures daga harkar samar da man fetur bayan kafa dokar PIA ta 2021, yana mai cewa hakan ya lalata tsarin tantance man da bin diddigin kuɗaɗen da ake samu.
Har ila yau, kwamitin ya nuna cewa babu kotu ta musamman da ke hukunta masu satar mai, yayin da rashin aiwatar da tsarin Host Communities Development Trust Fund (HCDTF) ke ƙara haifar da lalata albarkatun mai a yankunan Neja Delta.
Rahoton ya kiyasta cewa kuɗaɗen man da ba a bayyana inda suka shiga ba na iya kaiwa dala biliyan 300, yana kira ga gwamnati ta fara gaggawar dawo da su cikin gida da waje.
Kwamitin ya ba da shawarar a bai wa hukumar NUPRC ikon tabbatar da bin ƙa’idar ƙasa da ƙasa wajen auna man fetur a duk wuraren haƙowa da tashoshin fitarwa, ko kuma a dawo da sashen Weights and Measures cikin tsarin.
Haka kuma, ya buƙaci a ƙarfafa jami’an tsaro da kayan zamani kamar jiragen sintiri marasa matuƙa don bibiyar tashoshin mai kai tsaye da hana sata.
A cikin shawarwarin kwamitin akwai kafa Maritime Trust Fund da kotu ta musamman don hukunta masu satar mai cikin gaggawa, da kuma aiwatar da tsarin tallafa wa al’ummomin da ke da albarkatun mai domin rage ɓarna.
Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan rijiyoyin man da aka bari ba tare da kammala su ba a yankin Neja Delta, yana shawartar gwamnati ta bai wa matatun man ƙanana damar amfani da su don rage lalacewa da karuwar samar da mai a gida.
Duk da waɗannan matsaloli, rahoton ya nuna cewa an samu ƙaruwar samar da mai da kashi 9.5 cikin ɗari a shekarar 2023 — daga ganga miliyan 490.95 a 2022 zuwa ganga miliyan 537.57 a 2023.
