Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rt Hon Ya’u Umar Gwajo Gwajo wanda ya tattauna da manema labarai a Katsina a kan kasafin kudi da Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar,ya nuna gamsuwa musamman inda aka ware kashi 80 bisa 100 domin gudanar da manyan ayyuk.
Hon.Gwajo Gwajo wanda tsohon kakakin majalisar dokokin Katsina kuma a yanzu mai bai wa gwamna Shawara kan harkokin siyasa ya ce wannan tsari na nuna jajircewar Gwamna Raɗɗa wajen tabbatar da ci gaban jihar ta fuskar ababen more rayuwa da inganta tattalin arzikin jama’a.
Ya kuma jinjinawa Gwamnan bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da bunƙasa fannonin ilimi, lafiya da noma, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan da ke tabbatar da ɗorewar ci gaban al’umma.
A cewarsa, irin matakan da Gwamna Raɗɗa ke ɗauka wajen tallafa wa manoma sun sa su cikin farin ciki, domin a yanzu da dama daga cikinsu sun samu nasarori a harkar noma da kiwo.
Gwajo Gwajo ya kuma bayyana jin daɗin sa da goyon bayan da Majalisar Dokokin Jihar Katsina ke bai wa Gwamna Radda, wanda ya ce hakan yana taimakawa wajen sauƙaƙa gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa da ke amfani ga al’umma.
Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da ba gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya domin ta sami aiwatar da aikace-aikacen raya ƙasa.
