*Tinubu, ECOWAS, Chana, Gumi da rahoton BBC lauyan Amurka sun yi allawadai
*An yi musayar yawu tsakanin Akpabio da Barau
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayyar NIjeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da Gwamnatin ƙasar Amurka ta ɗauka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna take ’yancin yin addini.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Mohammed Idris (FNIPR), ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar ƙasa ta Yaɗa Labarai, Abuja, a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025.
Idris ya ce gwamnatin Nijeriya ta san irin damuwar da wannan mataki na Amurka ya haifar, musamman ma bayan furucin Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar kai farmaki kan Nijeriya bisa hujjar kariya ga Kiristoci.
Ministan ya jaddada cewa matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta ba su taɓa bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba, inda ya ce:
“Ta’addanci ba ya da addini, ba ya kallon ƙabila ko matsayi. Yaƙi ne da dukkan mutanen da ke son zaman lafiya a Nijeriya.”
Ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai na zahiri don kawo ƙarshen matsalar tsaro, kuma tun bayan hawansa mulki a watan Mayu 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsantsar niyyarsa ta tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.
A cewar Ministan, sojojin Nijeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda 13,500, tare da kama fiye da 17,000 da ake ci gaba da bincike da shari’a a kansu, haka kuma an ceto mutum 9,800 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.
Idris ya bayyana cewa sauyin da aka yi wa manyan hafsoshin tsaro da kuma sake tsara tsarin tsaro a ƙasar na daga cikin matakan Shugaba Tinubu na kawo ƙwarin gwiwa da inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.
“Manufar ita ce a tabbatar da cewa kowace kusurwa ta Nijeriya ta samu tsaro, kuma kowanne ɗan ƙasa ya rayu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.
Ministan ya kuma bayyana cewa an samu raguwar hare-haren ta’addanci sosai musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, tare da raunin kashi 80 cikin 100 na hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a Kudu maso Gabas.
Gwamnati ta ce an kama wasu manyan shugabannin ƙungiyoyin ta’addanci kamar Mahmud Muhammad Usman da Abubakar Abba na ƙungiyar Ansaru, da kuma Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargi da kitsa harin ofishin Majalisar ɗinkin Duniya a Abuja a 2011.
Ya ƙara da cewa mutum 125 daga cikin waɗanda ake zargi da ta’addanci sun riga sun samu hukunci, yayin da wasu ɗaruruwan ke ci gaba da fuskantar shari’a a kotuna daban-daban.
Duk da matakin Amurka, Ministan ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da Amurka da sauran ƙasashe domin kawar da ta’addanci, yana mai cewa:
“Muna fatan Amurka za ta fahimci cewa Nijeriya ƙasa ce mai girma, mai ɗimbin al’adu da addinai, wacce ke samun ci gaba a fannin tsaro da tattalin arziki.”
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya samar da jiragen yaƙi na Super Tucano da ake amfani da su wajen yaƙi da ’yan ta’adda, kuma nan gaba kaɗan ana sa ran ƙarin jirage masu sarrafa makamai za su iso ƙasar.
A ƙarshe, Idris ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tana mai cewa:
“Nijeriya tana hannun aminci da shugabanci mai cike da ƙwarin gwiwa. Shugaba Tinubu na jagorantar tsaro, ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya mai ɗorewa.”
An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump
An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya.
Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Nijeriya a matsayin “ƙasa Mai ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar.
Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Nijeriya na son jin matsayar Majalisar Dattawa kan lamarin.
Sai dai ya ce ba za a ɗauki matsaya ba har sai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da matsayinta a hukumance kan batun.
“Ni waye da zan mayar wa Trump da martani?” inji Akpabio cikin tambaya, yana mai bayyana cewa, Majalisar Dattawa ba za ta tattauna batutuwa ba sai an gabatar da su ta hanyar da ta dace.
Ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Nijeriya na son majalisar ta mayar da martani, za su jira bayanai a hukumance kafin su ɗauki mataki.
Sai dai kalamansa sun jawo martani kai tsaye daga mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin.
“Kar ka ji tsoro, ni zan yi magana. Ba na tsoron Trump. Zan faɗi ra’ayina,” inji Barau.
Ya ci gaba da cewa, “Ni ɗan Nijeriya ne, ɗan majalisa, kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa mai cikakken ’yanci. Ba na tsoron Trump. Kada ku ji tsoron Trump. Ku na da ’yancin faɗar ra’ayinku a kansa. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci. Yana yaɗa ƙarya game da ƙasarmu, kuma muna da ’yancin musanta hakan. Idan ka ce ba za ka yi magana ba, hakan daidai ne, amma abin da nake ƙoƙarin faɗa shine kada ka ji tsoron sa.”
Akpabio ya katse shi yana mai cewa, “Na ce ba na tsoro. Yaya za a ce Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa zai ji tsoron Trump?”
Ya ƙara da cewa, “Ka fahimta, ka faɗi ra’ayinka, amma kada ka bari mutane su danganta maka abin da ba ka faɗa ba. Amma idan ka na so na faɗa yanzu, zan faɗa. Amma ka saurara, zan faɗi abin da muka tattauna ne kawai.”
Daga nan sai Akpabio ya juya ga Akawun Majalisar, yana umarnin a goge kalaman Barau daga kundin rubuce-rubucen majalisar, yana mai cewa Barau ya “fita daga layin magana.”
Sai dai Barau bai nuna damuwa ba, ya tashi ya nufi kujerar Akpabio, inda suka yi gajeriyar raɗa da ta ja hankalin sauran ’yan majalisar, kafin ya koma kujerarsa.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, kalaman Trump da Sakataren Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, a shafin a ɗ cewa ƙasar na “shirin ɗaukar matakin soja,” sun haifar da fushi a fagen siyasa da diflomasiyya.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya musanta zargin Trump, yana mai jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya da ke ba da ’yancin addini da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Haka kuma, ƙasar China ta nuna rashin amincewa da kalaman Trump, tare da bayyana goyon bayanta ga Nijeriya, tana mai bayyana ta a matsayin “abokiyar”.
Chana ta gargaɗi Amurka
Beijing ta gargaɗi cewa babu wata ƙasa da ya kamata ta yi amfani da batun addini ko ’yancin ɗan adam a matsayin uzuri don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa mai ’yanci.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ce ta bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a birnin Beijing ranar Talata.
Ta ce: “China na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu yayin da take jagorantar al’ummarta kan tafarkin ci gaba da ya dace da yanayin ƙasar. A matsayinta na abokiyar hulɗa da Nijeriya, China tana adawa da kowace ƙasa da ke amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujja don tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe, ko barazanar amfani da takunkumi da ƙarfin soja.”
Mao ta ƙara da cewa China na marawa ƙasashen duniya baya wajen kare cikakken ikon kansu, tana mai cewa hanyar da ta fi dacewa ita ce tattaunawa cikin girmamawa da haɗin kai.
China na ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar tattalin arziki na Nijeriya, musamman ta fannin gine-ginen ababen more rayuwa, makamashi, da fasahar sadarwa.
Dangantakar ta ƙarfafa musamman ta hanyar shirin Belt and Road Initiatiɓe, wanda ya baiwa Nijeriya damar samun tallafi da lamuni don aiwatar da manyan ayyuka na raya ƙasa kamar jiragen ƙasa, tituna da tashoshin wutar lantarki.
Shugabannin ƙasashen Afirka da dama sun goyi bayan matsayin China, suna mai cewa kowace ƙasa na da ikon yanke shawara kan hanyarta ta ci gaba ba tare da tsoma bakin wasu ba.
Zargin kashe Kiristoci a Afirika shaci-faɗi ne, inji ECOWAS
ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas ta yi watsi da abin da ta kira iƙirarin ƙarya mai cike da hatsari da shugaban Amurka ya yi cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na far wa kiristoci tare da kashe su a Nijeriya..
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata ta ce irin wannan shaci-faɗi na Shugaba Trump ka iya ta’azzara matsalar tsaro tare da haifar da matsalar zamantakewa a yankin da dama ke fama da matsalar masu tsattsauran ra’ayi.
Ecowas ta jaddada cewa hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a yankin Afirka ta Yamma na shafar mutanen da ba su ji ba su gani ba, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ko jinsi ba.
Kan haka ne ƙungiyar ta buƙaci ƙasashen duniya su tallafa wa kowace ƙasa wajen yaƙi da ta’addanci da ke shafar kowa da kowa.
Da yiwuwar Trump na da taɓin hankali, cewar wani lauya a Amurka
Antonin sashen tsaro kuma tsohon mai bincike na matakin ƙasa da tarayya a Amurka, wato Ron Filipkowski, ya koka game da abinda ya kira da ‘daidaituwar hankalin’ Shugaba Donald Trump biyo bayan kalamansa na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya.
A wani rubutu ta shafinsa na ɗ a ranar Lahadi, Filipkowski ya ce ya dace a ce wasu lokutan “mu riƙa la’akari da cewa akwai yiwuwar yana da taɓin hankali.”
Sai dai, kalaman Filipkowski akan al’amarin ya tada hazo a Birnin Washington duba da yadda ake cigaba da tafka muhawara a tsakanin masana da sauran jama’a musamman bisa la’akari kasancewar Nijeriya jagora a Nahiyar Afirka ta fuskar tattali da yawan al’umma.
Masu sharhi akan lamuran siyasa sun bayyana iƙirarin Shugaban Amurkan na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya a matsayin abinda zai shafi al’ummomin ƙasashe da dama.
Nijeriya warki ce daidai ƙugun kowa – Fani Kayode kan barazanar kutsen Trump
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode ya ci alwashin cewa ‘yan Nijeriya za su iya jure wa dukkan wani barazanar soja da Amurka ke shirin ɗauka akan ƙasar bayan Shugaba Donald Trump ya umarci a fara shirin kai farmaki.
A wani rubutu ta kafar ɗ ranar Lahadi, Fani-Kayode ya yi alla-wadai da kalaman Trump yana mai bayyana shi a matsayin ‘azzalumin shugaba’ da ke yi wa Nijeriya barazana da tashin-tashina da mamaya.
Tsohon ministan ya ce wani aboki ya koka game da kalaman Trump, yana mai jaddada cewa ‘yan Nijeriya ba za su gudu su bar ƙasarsu ba, za su tsaya wajen kare ta matuƙar Amurka ta ƙaddamar da hari akanta.
Fani-Kayode ya kuma zargi Trump da ɗaukar matsaya biyu, inda ya zarge shi da kawar da kai akan abinda ake yi na kisan kiyashi a Sudan da Isra’ila yayin da yake yi wa Nijeriya ganin ƙasar da ake tauye ‘yancin wani addini.
Babu shugaban da zai bari ana kashe mutanensa – Wike
Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce ba zai yiwu ba a ce suna cikin gwamnati, amma kuma a riƙa yi wa Kiristoci kisan kiyashi, sannan su yi shiru.
Wike ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels a daren Litinin, inda ya alaƙanta zargin da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump da siyasa da aka ɗauka da zafi.
“Ta yaya za a ce gwamnati da nake ciki ne ake zargi da goyon bayan yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Wannan siyasa ce kawai da aka ɗauka da zafi,” inji shi.
Ya ce Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya Kirista ne, shugaban hukumar tsaron farin kaya Kirista ne, “sannan babban hafsan tsaron Nijeriya ma Kirista ne. Faɗa min, ta yaya mutum mai hankali zai yarda cewa za mu zauna a cikin gwamnatin da ke goyon bayan kashe mutanenmu.”
Wike ya ƙara da cewa babu shugaban da zai ji daɗi a riƙa kashe mutane a zamanin mulkinsa ko da kuwa daga ɓanngaren ƙasar.
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Nijeriya.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ne ga ’yancin Nijeriya.
“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” inji Gumi.
Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Nijeriya ta yanke hulɗa da Amurka.
“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” inji shi.
Gumi, ya kuma jaddada cewa Nijeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.
“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” inji Gumi.
Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi
Tsohon ɗan takarar Shugaban Nijeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Nijeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, abin damuwa ne da ke ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar.
Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na ɗ.
Obi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Nijeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali.
“Babu shakka Nijeriya na fama da matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma asarar dukiya.
“A cewar ƙungiyar Amnesty, aƙalla mutum 10,000 aka kashe a Nijeriya daga watan Mayun 2023, kuma kamar yadda na sha nanatawa, kashe-kashe a Nijeriya abin takaici ne, kuma abin Allah-wadai da ya zama dole a tashi haiƙan wajen magancewa.”
Obi ya ce za a iya magance matsalar ta hanyar samun shugabanci na nagari, “duk da cewa ba a wannan gwamnatin matsalar ta fara ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin takaɓus daga ɓangaren wannan mulkin na gwamnatin APC wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.”
Ya ce Nijeriya da Amurka suna da tarihin alaƙa da juna mai kyau, “kuma bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu.
“Wannan sabuwar dambarwar na buƙatar haɗakar diflomasiyya da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar.”
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin-kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ’yan ƙasa daga kowane yanki da addini.
Tinubu ya ƙara da cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ’yancin yin addini.
Za mu tallafa wa Nijeriya wajen yaki da ta’addanci – Chana
Jakadan China a Nijeriya, Mista Yu Dunhai, ya tabbatar da cewa, ƙasar Chana za ta ci gaba da tallafawa Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci.
Mr Dunhai ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na ɗ jiya Alhamis bayan ganawa da mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu.
Ya ce China “tana goyon bayan” gwamnatin Nijeriya a shirye-shiryenta na ci gaba waɗanda suka “daidai da gaskiyar ƙasar Nijeriya”.
Ya kuma ƙalubalanci tsoma bakin kowace ƙasa a harkokin cikin gida na Nijeriya “a ƙarƙashin hujjar addini da kare haƙƙin ɗan adam”.
“A matsayinta na babbar abokiyar hulɗar Nijeriya, Chana tana goyon bayan gwamnatin Nijeriya sosai wajen jagorantar mutanenta zuwa ga hanyar ci gaba da ta dace da gaskiyar ƙasar Nijeriya.
“Muna adawa da tsoma bakin kowace ƙasa a harkokin cikin gida na wasu ƙasashe a ƙarƙashin hujjar addini da kare haƙƙin ɗan adam. Muna adawa da barazanar takunkumi da amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.
“Chana tana son ci gaba da tallafawa Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin gida.”
Sai dai kuma, a wani nazari da kafar BBC ta gudanar ya kasa gano ingancin bayanan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da su wajen iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.
Kafar ta ce ta yi nazarin bayanan da take tunanin Trump ya yi amfani da su amma ta ce ta kasa tabbatar da alƙaluman.
Ta ce ta yi ƙoƙarin jin ta bakin waɗanda suka fitar da bayanan amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.
Kafar ta ƙara da cewa “ta gano cewa wasu alƙaluman da ake amfani da su wajen tabbatar da wannan zargi suna da wahalar tabbatarwa da rashin tabbas.”
