
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Shugaban Sojoji (mai ritaya), Laftanal Janar Abdulrahman Bello Dambazau, ya koka game da yadda al’amarin taɓarɓarewar tsaro ke cigaba da ta’azzara a yankin arewacin Nijeriya, yana mai gargaɗin cewa ƴan bindiga da mayaƙa sun koma karɓe iko da wasu garuruwa.
Da yake jawabi a babban taron harkokin jarida da tsaro da aka yi a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi a ranar Litinin, Dambazau ya ce shiyyar tana fama a matsanancin barazanar tsaro na tsawon sama da shekaru 20, inda a yanzu al’amarin ya yi ƙamari.
A cewarsa, yanzu ƴan ta’adda sun daina taƙaita da garkuwa da kashe-kashe, har sun kai matakin ƙaƙaba haraji, gudanar da al’amuran yau da kullum da sanya dokoki ga mazauna yankunan da suka karɓe iko da su.
Tsohon shugaban sojojin ya bayyana cewa waɗannan ƙalubale yanzu a bayyane suke a yankunan Arewa, yana mai bada misali da kashe-kashe a masallatai a jihohin Katsina, Borno, Zamfara da Kano.
Haka kuma akwai ɗaiɗaita al’ummomi, lalata al’amuran tattali, faɗa tsakanin manoma da makiyaya da harkar satar mutane, lamuran da suka yi sanadin halaka dubunnan jama’a da ɗaiɗaita miliyoyi.
Dambazau, ya bayyana inganta harkokin tattalin arziƙi acikin al’umma shi ne babban abinda zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa rage talauci shi zai sanya a samu sauƙi a harkar rashin tsaro matuƙar jagorori suka tsaya a kai.
