
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo a watan nan na Nuwamba.
Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam’iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban da ake ciki.
Haka kuma kotun ta hana INEC sa ido akan babban taron ko kuma amincewa da sakamakon taron wanda ake sa ran fitar da sababbin shugabannin jam’iyyar.
Saidai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a Jihar Oyo ta umarci jam’iyyar da ta cigaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar da ruɗani.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a yau Talata, bayan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamiɗo ya shigar da ƙara, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Lamiɗo ya shigar da ƙara ne yana buƙatar kotun ta dakatar da jam’iyyar daga zaɓen fitar da sababbin shugabanni, inda ya ƙalubalanci abinda ya kira da hana shiga takarar da ya ce an yi masa.
