Kano: An yi wa karnuka fiye da 130 allurar riga-kafi a Bichi

Spread the love

Karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano ta gudanar da allurar riga-kafin ciwon haukan karnuka a yankin Gadar ‘Yan Goro titin FCE, inda wani baƙon kare ya ciji yara uku.

Kansilan sashen kula da gona na yankin, Hon. Usman Muhammad Charity, ya ce karnuka sama da 130 na kimanin mutane 92 aka yi wa allurar rigakafin ciwon haukan kare a kewayen da tsautsayin cizon ya wakana ga matasa.

A sanarwar da Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, wato jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar ta fitar, Kanslina ya kuma yaba wa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa namijin ƙoƙarinta na samar da Ma’aikatar Habaka Kiwon Dabbobi a Kano, domin kula da bada kariya daga cututtukan da ka iya haifar da gagarumar matsala a cikin al’umma.

Sannan ya jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, bisa rawar ganin da ya taka wajen samar da allurar riga-kafin da aka yi wa waɗanda abin ya shafa domin ceto lafiyarsu tare da riga-kafin da aka yi wa karnukan domin kawar da annobar ciwon.

“Waɗannan karnuka ba wai iya na mafarauta ba ne, hatta masu kiwonsa domin sha’awa ko gadi a gida su ma sun kawo, akwai wanda saboda gata ma a motarsa yana shan AC ya kawo shi aka yi masa.”

A jawabin likitan Asibitin Dabbobi mai Kula da Shiyyar Dambatta, Dakta Salisu Ali Alhassan, ya yi bayanin irin illar cutar haukan kare a cikin al’uma, muddin yawun karen da yake dauke da irin wannan cutar ya shiga jikin mutum ko wata dabba ta hanyar cizo, a nan cutar take shiga jinin jikin wanda ya ciza, kuma idan ba a yi magani da taka-tsantsan ba cutar na iya yaɗuwa a cikin al’umma.

“Shi ya sa gwamnati ta ba da ainahin dama a zo a samu wadannan karnukan da suke a cikin garin Bichi a yi musu rigakafi, wanda ko da wani karen ya shigo ya,sake cizon su, in sha Allahu karnukan ba za su kamu da wannan cutar ba.”

Ɓangaren mafarauta da suka yi juyayin wannan al’amari, mai dawa Jibrin Dangimbo Zango, ya yi kira ga ma’abota kiwo, musamman karnuka, su rika kai su rigakafi a duk lokacin da ake yi musu bisa doka, idan kuma mutum ya san ba zai iya ba to ya bai wa wanda zai iya jimirin ɗawainiyar kiwon yadda yakamata a dokance.

Ya ce, matuƙar ba haka ba, idan karensa ya ciji mutum, to doka za ta yi aiki akansa domin hukuma ba za ta bar shi ba.

“Ko’ina ana faɗakarwa ana gaya wa mutane ko cizon wani su ka yi idan ba ka yi musu rigakafi to za ka samu matsala, shi ya sa muke kawo su ake yi musu allurai” inji Mai dawa Jibrin Dangimbo Zango.

“Masu alamun ciwon, yanayin tafiyarsu za a ga kansu yana gilu-gilu haka, da sun ga mutum suke kai masa wawura su cije shi.” Umar Yusuf Bichi.

“Kamar yadda za mu kula da ‘ya’yanmu haka za mu kula da su, tun da dabbobi ne ba baki gare su ba”, inji Madanu Muhammad Bichi.

By Babaji