
Kungiyar ƴan kasuwa ta ‘Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited’, sun miƙa saƙon godiya da girmamawa ga ɗan Majalisar Wakila mai wakiltar mazaɓar Bichi Hon. Dk. Abubakar Kabiru Abubakar Bichi.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale ne ya bayyana saƙon da ƙungiyar ta miƙa zuwa ga ɗan majalisar.
Ƙungiyar ta mika saƙon da girmamawar ne ga ɗan majalisar akan hanyarsa ta fita daga garin Bichi, bayan ya halarci taron rantsar da ɗalibai da kuma gabatar da gaishe-gaishe bisa rashe-rashen da aka yi a ƙaramar hukumar.
Tun da fari, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, ya bayyana wa ‘yan kasuwar zaman da suka yi da ɗan majalisar a Abuja bisa alƙawarin da ya yi musu na irin gudunmawar da zai ba su domin haɓaka kasuwanci da tattalin arzikinsu.
Lamarin da ya sa suka ga ya dace su fito domin su nuna jin daɗinsu da godiyarsu a gare shi tare da masa fatan alheri, sakamakon cika musu wannan alƙawari da ya yi tun kafin a rushe kasuwar.
A makon da ya gabata ne aka yi zama da shugabannin kasuwar domin duba matsalolin kasuwar tare da magance su, inda tsarin ba da jarin zai shafi mazauna cikin kasuwar ne masu cin kasuwar yau da kullum domin bunkasa ta.
A nasa jawabin Hon. Abubakar kabiru Abubakar, ya nuna farin ciki da jin dadinsa bisa wannan girmamawa da ‘yan kasuwar suka yi masa.
A karshe Hon. Abubakar Kabiru Abubakar, ya yi fatan alheri da addu’ar samun ci-gaba mai ɗorewa a kasuwar ta Kabiru Abubakar Ultra-Modern Market Bichi, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta bayyana a wata takarda.

