Kano: UNICEF ta jagoranci taron wayar da kan al’umma akan yi wa yara rijistar haihuwa a Bichi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An gudanar da taron wayar da kan jama’a game da mahimmancin yi wa yara rijistar haihuwa da zarar an haife su kafin kwana 60 a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano.

Taron ya haɗa da kananan hukumomin Bichi, Ɓagwai, Ɗambatta, Ghari da Tsanyawa domin kawo sauyi ga al’ummar jihohin arewa dangane da yanayin koma-bayan da suke ciki a fannin yin rijistar haihuwa, musamman yakunan karkara ta Kano.

Malam Usman Yahya, wanda ƙwararren jami’i ne a ofishin Hukumar UNICEF ya ce, hakan yana tauye kuɗi da albarkatun kasa da ake tura wa kowace jiha sakamakon ana tattara adadin yawan jama’a a kowane yanki ta hanyar bayanan rijistar haihuwa.

Ya kuma ce, takardar haihuwa ita ce ƴancin kowane ɗan ƙasa domin da ita ake tabbatar da kasancewar mutum wajen ba shi, tsaro, kariya da sauran hakkokinsa kacokan a gwamnatance.

Akan haka ya ja hankalin al’umma musamman iyaye wajen kiyaye wannan haƙƙi domin tseratar da yara daga matsaloli da ƙalubalen rayuwa na tauyewar haƙƙoƙinsu.

Kazalika, ya ce a matakin ƙasa Nijeriya ma da take da yawan jama’a kaso dari cikin dari na adadin yara ‘yan kasa da shekara daya, a halin yanzu wadanda suke a kayyade kaso arba’in cikin dari ne, don haka wajibi ne al’uma su dukufa yi wa yara rijistar haihuwa domin a sauya wannan alƙaluman.

“Misali jihar Kano, a ce za a gina makarantu dubu goma, rijistar haihuwa ake dubawa domin ganin yiwuwar hakan.”

Haka ma jami’in Hukumar Wayar da Kai ta Kasa da ke nan jihar Kano, Malam Balarabe Yusuf Sani, ya koka bisa ƙananan hukumomin da suke fuskantar kalubale sakamakon wofantar da rijistar haihuwa a baya, wanda a halin yanzu suke fuskantar matsalar gaza biyan ma’aikatansu albashi, dalilin kasafin da ake tura musu bisa ƙarancin waɗanda hujjar rijistar haihuwa ta ƙayyade a yankunansu.

Shi kuwa Malam Ibrahim Magaji, jami’in Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ya sake tabbatar da mahimmancin yin rijistar haihuwa a hukumarsu, inda ya ce, da ita ake amfani duk inda mutum zai shiga a duniya bangaren karatu, aikin hajji, umara da sauransu.

Ya kuma sanar da cewa, yara ‘yan shekara 1 zuwa 17 hukumar tana yi musu rijistar haihuwar ne kyauta, amma idan suka haura haka sai dai a hedikwatarsu kuma sai an biya kuɗi.

Yara ƙasa da shekara daya kuma shugabannin wakilan mazaɓu ne suke yi musu kyauta a mazabunsu, sannan ya yi bayani a yanzu an alakanta rijistar haihuwa da katin ɗan ƙasa, duk wanda ya kai yaronsa yin rijistar haihuwa, da bayanansa na katin dan kasa ake amfani.

By Babaji