Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Ranar 12 ga watan Nuwamba ana gudanar da bikin Ranar Masu ɗaukar Hoton Cututtuka ta Duniya (World Radiography Day), wacce ke tunawa da samuwar hasken ɗ-ray da ake amfani da shi wajen gano cututtuka daban-daban a faɗin duniya. A wannan rana, ana kuma gudanar da taruka da horo domin kara ilimi, kwarewa da sanin sabbin fasahohi ga ma’aikatan fannin ɗaukar hoton cuta.
A bana ma, ƙungiyar Masu ɗaukar Hoton Cuta ta ƙasa (ARN), reshen Jihar Kano, ta gudanar da nata bikin a dakin taro na Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano (AKTH), inda masana, likitoci da jami’an lafiya daga manyan asibitoci suka halarta. Cikin wadanda suka halarci taron akwai wakilai daga Asibitin Murtala Muhammad, Asibitin Muhammad Abdullahi Wase, da Farfesa Abdurrahman Sheshe, shugaban asibitin AKTH.
A jawabinsa, Dakta Muhammad Sajo, daya daga cikin kwararrun likitoci a fannin, ya bayyana cewa manufar wannan rana ita ce tunawa da ranar da aka gano hasken ɗ-ray, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gano cututtuka da kuma taimakawa wajen inganta magani. Ya ce, “Hasken ɗ-ray ya zama ginshikin bincike da magani, domin ana amfani da shi wajen gano kusan kowacce irin cuta a jikin mutum.”
Shi ma Dakta Abdurrahman Abubakar Gushi, wanda ke aiki a asibitin AKTH, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin karfafa zumunci da hadin kai a tsakanin ma’aikatan fannin, tare da wayar da kan jama’a game da irin rawar da masu daukar hoton cuta ke takawa wajen kula da lafiyar al’umma.
Dakta Gushi ya kara da cewa irin wannan biki na kara ilimi da fasaha ga ma’aikata, tare da samar musu da sabbin hanyoyin gudanar da aikinsu cikin inganci. Ya ce, “Wannan rana ce da ke bawa ma’aikatan damar musayar sani da kwarewa domin kara inganta harkar lafiya.”
Taken bikin bana shi ne: “ƙarfafa Ma’aikatan Daukar Hoton Cuta Don Inganta Kiwon Lafiya.” Taken ya mayar da hankali ne wajen karfafa gwiwar ma’aikatan fannin, tare da kara musu horo da ilimi domin ci gaba da bunkasa harkar lafiya a Jihar Kano da kasa baki daya.
