Gwamna Abba ya lashe lambar girmamawa a bikin finafinan Abuja karo na 22

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

A wani gagarumin biki na 22nd Abuja International Film Festival, an karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta musamman (Distinguished Merit Award) saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban masana’antar ƙere-ƙere da fina-finai, musamman Kannywood.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Harkokin Musamman na Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, Sani Abba Yola, ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa bikin bada kyautar ya gudana ne a Abuja, inda ya tara manyan masu shirya fina-finai, daraktoci, jarumai da sauran ‘yan masana’antar nishaɗi daga cikin gida da ƙasashen waje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu wakilci a wurin taron daga Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da Sakataren Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Abba Almustapha; Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, Hon. Sani Musa Danja; da Shugaban Gidauniyar Kannywood, Alhaji Ahmed Alkanawy, da sauransu.

A yayin miƙa lambar yabo, Dr. Fidelis Duker, wanda shi ne wanda ya kafa Abuja International Film Festival, ya bayyana cewa an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin kyawawan ayyukan da ya aiwatar don farfaɗo da harkokin Kannywood.

Ya ce cikin ayyukan da suka ja hankalin kwamitin akwai shirya horo ga fiye da ‘yan Kannywood ɗari guda (100), samar da kayan aiki ga wasu jarumai, da kuma gyara dokokin Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano don dacewa da zamani.

Dr. Duker ya kuma yi kira ga sauran gwamnonin ƙasashen Najeriya da su kwaikwayi Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen samar da manufofi da shirye-shiryen da za su bunƙasa masana’antar kere-kere don faɗaɗa tattalin arziƙin jihohinsu da ƙasar baki ɗaya.

Da yake karɓar lambar yabo a madadin Gwamnan, Kwamishina Waiya ya bayyana farin ciki da girmamawar, yana mai cewa hakan hujja ce ta irin namijin ƙoƙarin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi wajen haɓaka sashen kirkira da nishaɗi a jihar.

Ya ƙara tabbatar da cewa Gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗin gwiwa da masu shirya Abuja International Film Festival domin ƙara bunƙasa masana’antar kere-kere a Kano da Arewacin Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi