Sarkin Kabin Argungu ya ’yanta fursunoni 12

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

A cikin shagalin murnar cikarsa shekaru 29 da hawa karagar mulkin daular Masarautar Kabin Argungu, Mai Martaba Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya ziyarci gidan yari mai matsakaicin tsaro da ke garin Argungu, inda ya ‘yanta fursunoni 12 masu ƙananan laifuka da kuma waɗansu da wannan wannan shi ne karon farko da aka tsare su.

Da ya ya ke jawabi a yayin ziyarar, mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, bayan addu’o’i na musamman ga waɗanda ke tsare a gidan ya kuma ya hankalin su a matsayin su na Musulmi da su mayarda duk abinda ya same su a matsayin ƙaddarowa ce daga Mahalicci, ya kuma yi addu’ar Allah ya sanya wannan jarabawar ta zame musu kaffara.

Bayan wannan kuma basaraken ya ƙara da cewa kamar yadda aka saba kowace shekara ya kan ziyarci wannan gidan musamman a irin wannan lokacin na bikin zagayowar ranar sarautar sa duk da ya ke yana kulawa da wannan gidan ba sai irin wannan lokacin ba sai dai a irin wannan lokacin ya kan yi tattaki da kan sa har gidan domin ziyara da kuma bayar da abin da ya saba da hannunsa.

A wannan ziyarar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya fanshi fursunoni 12 da aka tsare sanadiyyar ƙananan laifuka da kuma waɗansu da wannan shi ne karo na farko da aka tsare su kuma musamman a kan bashi da ba mai tsanani ba ne.

Haka-zalika ya kara da cewa yanzu haka akwai waɗansu mutane goma sha uku da ke da matsalar bashi da in Sha Allahu zai bi hanyoyin da za nemo musu mafita saboda su ma su koma su cigaba da rayuwa da iyalan su da sauran abokan huldodin su ma yau da kullum.

 Da ya ke jawabi tun farko, shugaban gidan gyaran hali mai matsakaicin tsaro da ke garin Argungu Sufurtanda Lauwal Yeldu, ya yana wa Basaraken bisa ga irin kulawar da ya ke baiwa wannan gidan.

Ba shakka mai martaba ya nuna shi UBA ne kuma jagora da ya ɗauki kowa na sa ne saboda duk wanda ke gidan nan yana sane da irin gudummawar da ya ke baiwa lokaci zuwa lokaci kuma uwa-uba kowace shekara ya kan ziyarci wannan gidan tare da kawai kayan abinci da na sauran buƙatocin rayuwa.

Sufurtanda Lauwal Yeldu ya bayyana cewa a matsayin sa na ɗan asalin wannan masarautar na farko da ya fara rike wannan gidan shi ma in Sha Allahu zai himmatu wajen ganin ya bar tarihi ta yadda ba za a manta da shi ba.

Ya kuma yaba wa gwamnan Kebbi Malam Nasir Idris da Mataimakin sa Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi bisa ga hadin kai da suke ba shi a duk lokacin da ya zo da wata bukata da ta shafi gidan wanda sanadiyyar haka yanzu an zamanantar da gidan ta hanyar saka waɗansu na’urori  don tabbatar da samun tsaro daga cikin su kuma akwai tabbacin samun wutar lantarki sa’o’i ashirin da huɗu.

By ukarofi