Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta hana wasu ‘yan ci-rani 332 shiga ƙasar nan ta iyakar Seme, bayan da aka gano ba su da sahihan takardun tafiya.
Kwamturola Janar ta Hukumar, Kemi Nandap, ce ta bayyana haka a Abuja ranar Talata, yayin taron wayar da kai ga masu ruwa da tsaki mai taken “Evolving Patterns in Smuggling of Migrants: Towards a Coordinated National Response.”
Nandap ta ce, hukumar ta ƙarfafa tsarin doka da horar da jami’anta don ƙara inganta bincike da hana harkar safarar mutane da shige da ficen ba bisa ƙa’ida ba.
“Kwanan nan jami’an sintirin iyaka a Seme sun hana wasu ‘yan ci-rani 332 shiga Nijeriya saboda rashin sahihan takardun tafiya.
Haka kuma, an daƙile wasu ‘yan Nijeriya 294 da ake zargin suna ƙoƙarin barin ƙasa ta hanya ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin abin da ake kira ‘Japa Syndrome’,” inji ta.
Ta ƙara da cewa, an kuma ceto mutane 36 da suka haɗa da waɗanda aka yi wa safarar mutane da yara maza da mata da ke aikin wahala, sakamakon amfani da sabbin na’urorin CCTV da aka girka a wuraren da ake sa ido.
Nandap ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na yankuna irin su AU, ECOWAS, EU, IOM, UNODC, INTERPOL, da ‘yan sanda na Jamus, domin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar tsaro.
“Yaƙi da safarar ‘yan ci-rani ba kawai batun tsaro ba ne — alhakin ɗabi’a ne. Kowanne mutum da aka safarce shi rayuwa ce da ke cikin haɗari, kuma iyali ne da aka tarwatsa,” inji ta.
Ta kuma kira hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ƙungiyoyin farar hula da masu zaman kansu da su ƙara haɗin kai, tana mai jaddada cewa babu wata hukuma guda da za ta iya yaƙi da safarar ‘yan ci-rani ita kaɗai.
“Nasaramu tana dogara ne da aiki a matsayin ƙasa ɗaya mai tsari da gaskiya, inda mutunci da kare rayuwa suka zama ginshiƙi. Dole mu gina Nijeriya inda hanyar tafiya ta halal da amintacciya ta zama al’ada,” inji ta.
