Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta sanar da samun gagarumar nasara a gyaran tsarin kiwon lafiya, inda ta ce an samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu da kashi 17%, tare da raguwar mace-macen jarirai da kashi 12% a faɗin ƙasar, musamman a cikin ƙananan hukumomi 172 da ke da matsalar yawan mace-mace.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na ma’aikatar da aka gudanar a Abuja, ranar Laraba.
Farfesa Pate ya bayyana cewa, za a gudanar da Bita na Shekara-shekara na haɗin gwiwa domin tantance cigaban da aka samu a bangaren lafiya, da sabunta alƙawuran gaskiya da ɗaukar nauyi, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati ta tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi ƙarƙashin Shirin Sabon Jari a Sashen Lafiya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar a 2023.
A cewarsa, daga cikin muhimman ma’aunin aiki 41 (KPIs) da aka sanya karkashin shirin gyaran lafiya na shugaban ƙasa, 37 sun riga sun cimma nasara – abin da ya kira “gagarumar ci gaba” sakamakon daidaituwar manufofi tsakanin gwamnati ta tarayya da ta jihohi.
“A karo na farko, muna ganin yadda jihohi da tarayya suka haɗa kai wajen aiwatar da tsare-tsaren aiki na shekara, bisa tsarin da ya yi daidai da burin ƙasa baki ɗaya,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa, an tura masu aikin lafiya na musamman 774 zuwa dukkan ƙananan hukumomi a ƙasar, sannan jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya sun gudanar da nazarin ayyukan lafiyarsu, tare da halartar jama’a wajen yanke shawara.
A ɓangaren kula da lafiya, gwamnatin ta ce an samu ƙaruwa a yawan mata masu zuwa duba lafiya kafin haihuwa (antenatal care), ƙaruwa a haihuwa ta hannun ƙwararrun ma’aikatan lafiya, da kuma ƙarin amfani da dabarun tsara iyali.
Haka kuma, yawan mutanen da suka nemi kula a cibiyoyin lafiya na farko ƙarƙashin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) ya tashi daga ziyara miliyan 10 a farkon 2024 zuwa miliyan 45 a zangon biyu na 2025 — alamar cewa amincewar jama’a da sabis na gwamnati na ƙaruwa.
Ministan ya ce, wannan ci gaban yana nuna cewa shirin gwamnati na sabunta sashen lafiya yana fara haifar da sakamako kai tsaye ga rayuwar al’umma, musamman mata da yara masu fama da rashin kula a yankunan karkara.
