Manufofin Tinubu za su daidaita arzikin Nijeriya mai ɗorewa – CBN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa — duk da cewa suna haifar da ƙalubale na ɗan lokaci — suna da matuƙar muhimmanci wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar bisa turbar ci gaba mai ɗorewa.

Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Abuja, yayin gabatar da jawabin buɗe taro a taron shekara-shekara na manyan jami’an CBN na 2025, mai taken “Deepening Reforms: Path to Diversification and Sustainable Growth.”

Ya ce, taken taron ya zo a lokaci mai muhimmanci kuma yana da ma’ana, ganin yadda tattalin arzikin duniya ke canjawa, abin da ya sa ake buƙatar ƙarfafa sahihancin manufofi, gaskiya a kasuwanni, da kyakkyawan tsarin gudanarwa.

“Manufofi masu sahihanci, kasuwanni masu gaskiya, da ingantaccen tsarin mulki suna janyo sahalewar masu zuba jari. Wannan ne ya sa muka fara ganin dawowar kwarin gwiwar masu saka jari a kasuwanninmu,” inji shi.

Cardoso ya ce, babban ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin Nijeriya shi ne tsayar da farashi (price stability) da kuma manufofin da ke nufin daidaita hauhawar farashin kaya (inflation targeting) domin ƙara tabbaci, daidaita tsammanin kasuwa, da kuma ƙarfafa jarin dogon lokaci.

A nasa ɓangaren, ƙaramar Ministar Kuɗi, Dr Doris Uzoka-Anite, ta bayyana cewa ma’aikatarta na haɗin kai sosai da CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arzikin ƙasa.

Ta ce, “Ma’aikatar kuɗi da CBN su ne ginshiƙan da suka keɓance tsarin tattalin arzikin Nijeriya. Su ne ginshiƙan da ke tura tattalin arzikinmu zuwa ga haɓaka, ƙarin samar da aiki, da ƙarfafa gasa ta dogon lokaci.”

Ministar ta kuma bayyana cewa gwamnati na da burin ƙara GDP zuwa sama da kashi 4 cikin 100 a shekara kafin 2027, tare da fatan ninka girman tattalin arzikin ƙasar zuwa dala biliyan 750 nan da shekarar 2037.

Ta ce, idan aka ci gaba da samun ci gaban tattalin arziki a matsakaicin kaso 7% a shekara, hakan zai iya ninka darajar tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru goma sha biyu masu zuwa.

By ukarofi