
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗa Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin cigaba da jagorantar hukumar na tsawo wasu shekaru biyar nan gaba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda, yau Juma’a.
A watan Junairun shekarar 2021 ƙarƙashin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, aka fara naɗa Marwa a matsayin shugaban NDLEA bayan zama shugaban kwamitin shawarwari akan yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga 2018 zuwa Disambar 2020.
Sake naɗa haifaffen Jihar Adamawan kuma tsohon jami’in soja ya nuna cewa zai cigaba da jagorantar hukumar har zuwa nan da shekarar 2031.
Buba Marwa, wanda tsohon gwamna ne na zamanin mulkin soji a jihohin Legas da Borno, ya yi karatunsa a makarantun sojoji na Nigerian Army Military da Nigerian Defence Academy (NDA).
Haka kuma, ya yi karatun digiri na biyu har sau biyu a jami’o’in University of Pittsburgh daga 1983 zuwa 1985 a fannin harkokin hulɗa da jama’a da na ƙasa-da-ƙasa, da kuma fannin nazarin hulɗa da jama’a a Havard University daga 1986 zuwa 1986.
A matsayinsa na shugaban NDLEA, hukumar ta yi nasarar kama mutane 73,000 masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da ƙwato sama da kilogram miliyan 15 na miyagun ƙwayoyi.

