Matan sojojin da suka mutu na neman agaji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar Tsofaffin Sojoji ta Nijeriya ta buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace.

Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi.

Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta.

Allison-Alamini ya kuma sha alwashin ba da muhimmanci ga walwalar tsoffin sojoji a jihar, tare da gode wa mambobin ƙungiyar bisa yadda suka ba shi amanar shugabanci.

Zaben ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya, ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Bello Kaya, tare da wakili daga ofishin sakataren gwamnatin jihar.

A yayin zaben, Odon Alfred ya sake lashe mukamin mataimakin shugaban ƙungiyar ba tare da hamayya ba, yayin da Mista Amiekumo Angozi ya zama ma’ajin ƙungiyar.

Shugaban kwamitin zaɓe, Mista Aghomo Samson, ya bayyana zaɓen a matsayin mai cike da kwanciyar hankali, gaskiya da amana. Ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa halin natsuwa da suka nuna kafin, yayin, da bayan gudanar da zaɓen.

Ya ya buƙaci sabbin shugabannin da su jagoranci ƙungiyar cikin adalci ba tare da rikici ba, tare da haɗa kan dukkan matakan kungiyar a cikin dukkan al’amuransu.

Wakilin sakataren gwamnatin Jihar Bayelsa, Ogori Raymond, ya buƙaci sabbin shugabannin su gudanar da mulki mai inganci, gaskiya da gaskatawa, wanda zai ƙarfafa zumunci, haɗin kai, adalci da daidaito a tsakanin mambobin ƙungiyar.

A nasa ɓangaren, wakilin shugaban ƙasa na majalisar ƙungiyar tsoffin sojoji ta Nijeriya, Mista Toye Dele, ya sake tabbatar da ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kula da walwalar tsoffin sojoji da kuma kiyaye gado da tarihi na rundunar sojojin Nijeriya.

By ukarofi