Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa, Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana cewa ta kula da yara masu fama da rashin abincin dake gina jiki mafi yawa a Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar Ahmed Aldikhari ya ce likitocin kungiyar sun kula da yara kusan 300,000 dake fama da matsalar a jihohin dake Arewacin Nijeriya a shekarar 2024.
Aldikhari ya faɗi haka ne a taron tattauna hanyoyin yakan yunwa a jikin yara ƙanana a jihar Katsina da jihohin dake Arewa maso Yamma wanda gwamnatin jihar Katsina da MSF suka shiyar Kuma aka yi ranar Alhamis a Abuja.
Mataimakin Shugaban ƙasa Kashin Shettima na daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron inda yake cewa rashin abinci mai gina jiki ga yara a matsayin matsalar dake cutar da al’umma a hankali inda kafin a ankara Nijeriya ta yi asarar Dala biliyan 56 duk shekara.
Shettima wanda mai bashi shawara kan harkokin kiwon lafiya Uju Rochas-Anwukah ta wakilce shi a taron ta ce mataimakin shugaban kasan ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen kawo karshen rashin abinci mai gina jiki sai dai Kuma ya yi gargaɗin cewa rashin gaggauta ɗaukan mataki kan iya shafan makoran kasan ta hanyoyin da basu kamata ba.
“Idan yaro baya girma saboda rashin abinci mai gina jiki hakan ka iya shafan makomar mu a ƙasar mu Nijeriya.
“Duk kuɗin da aka saka domin samar da abincin dake gina jiki ba asara ba ne amma dabara ce da zai taimaka wajen samar wa kasan makomar mai kyau domin duk dala daya da aka saka domin yakan matsalar ana samun riban dala ishirin da uku.
Ya kuma ce gwamnati na nan kan bakinta na amfani da shirin yakan rashin abinci mai gina jiki a duk ƙananan hukumomin dake ƙasar nan.
Shettima ya yi kira ga shugabanin da su tabbatar zaman da suka yi zama ne da zai sa a ɗauki matakan da za su taimaka wajen kawar da matsalar rashin abincin dake gina jiki a ƙasar nan.
Raddah ya ware naira biliyan 14 don inganta lafiya da gina masana’antar hada RUTF.
A tsokacin da ya yi a taron Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ta matsa daga wayar da kan mutane zuwa yakan matsalar.
Ya ce gwamnatin sa ta ware naira biliyan 14 domin inganta fannin lafiya a 2024.
Raddah ya ce sauran matakan da gwamnati ta ɗauka sun haɗa da biyan naira biliyan ɗaya cikon kuɗin haɗin gwiwar yaƙan yunwa a jikin yara ƙanana da gwamnati ta ke yi da Asusun UNICEF wanda suka fara daga 2023 zuwa 2025.
Gwamnati ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 260 da manyan asibitoci bakwai a jihar.
Gwamnati ta ɗauki jami’an Lafiya 1,600 sannan ta saka mutane musamman matasa galihu cikin tsarin inshorar lafiyar jihar.
Raɗɗah ya ce gwnati na Shirin Bude masana’antar haɗa maganin RUTF da garin kunnu na ‘Tom-Brown’ a jihar.
“Buɗe masana’antar zai taimaka wajen samar wa yara abincin gina jikin su, samar wa matasa aiki da inganta tattalin arzikin jihar.
Ya kuma ce gwamnati za ta yi ƙoƙari domin ganin ta fara amfani da dokar kare haƙƙin yara kanana domin rashin kare haƙƙin yara na daga cikin matsalolin da ya sa ake samun yaran dake fama da matsalar rashin abincin dake gina jikinsu.
