Kyakkyawan shugabanci shi ne ginshiƙin cigaban aiki – Musa Makama

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An bayyana cewa kyakkyawan shugabanci da jagoranci nagari sune ginshiƙan samun ci gaba a kowanne wurin aiki. 

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Daraktan Mulki na ƙaramar Hukumar Minjibir, Alhaji Ahmad Musa Makama, a lokacin da Cibiyar Wayar da Kan Al’umma da Kyakkyawan Shugabanci ta karrama shi da lambar yabo saboda jajircewarsa wajen gudanar da aiki da gaskiya da rikon amana.

An gudanar da bikin karramawar ne a ofishin Daraktan dake sakatariyar karamar hukumar Minjibir, ranar Litinin da ta gabata. A yayin taron, Alhaji Makama ya bayyana cewa nasara da ci gaba a wurin aiki ba ya samuwa sai da hadin kai tsakanin ma’aikata da shugabanni. Ya ce, “Idan akwai kyakkyawan shugabanci da fahimtar juna, to tabbas za a samu ci gaba da ingantuwar ayyuka a kowanne mataki.”

Da yake tsokaci kan lambar yabon da aka bashi, Daraktan ya bayyana farin cikinsa tare da nuna godiyarsa ga cibiyar da ta zabe shi daga cikin daraktocin mulki 44 da ke fadin jihar Kano. A cewarsa, “Na ji dadi matuka saboda wannan yabo ya nuna an lura da kokarinmu wajen inganta harkokin mulki da ayyukan ma’aikata.”

Alhaji Makama ya kuma godewa Shugaban Karamar Hukumar Minjibir, Hon. Jibrin Nalado Kunya, da sauran ma’aikata bisa hadin kai da goyon bayan da suke bashi wajen gudanar da aikinsa. Ya ce, “Da ba don hadin kan ma’aikata da goyon bayan shugaban karamar hukumar ba, da wannan yabo bai samu ba. Wannan nasarar ta kowa ce, ba tawa kawai ba.”

Daraktan ya ƙara da cewa wannan karramawar za ta kara masa kwarin gwiwa wajen aiwatar da ayyuka masu tasiri ga ci gaban garin Minjibir da bunkasar tattalin arzikin al’umma.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) reshen Minjibir, Kwamared Saifullahi Tijjani Minjibir, ya ce sun karbi wannan labari da murna, domin tun bayan zuwan Daraktan, an samu sauye-sauye masu amfani a fannoni daban-daban. Ya ce, “A dan kankanin lokacin da ya dauka a ofis, an ga bambanci. Mutum ne mai san aikin sa, kuma ko shugaban karamar hukuma baya nan, ayyuka na ci gaba yadda ya kamata.”

Shi ma Shugaban Cibiyar Wayar da Kan Al’umma da Kyakkyawan Shugabanci, Kwamared Auwalu Yalwa, ya bayyana cewa sun zabi Alhaji Makama ne saboda jajircewarsa da adalci wajen kula da ma’aikata da tabbatar da gaskiya a wurin aiki. Ya kara da cewa, “Muna fatan wannan yabo zai kara masa kwarin gwiwa wajen ci gaba da hadin kai da ma’aikata domin cimma manufofin gwamnati.”

Taron karramawar ya gudana cikin natsuwa da farin ciki, inda ma’aikata da shugabanni suka yaba da irin nagartar da Daraktan ke nunawa a aikinsa, suna mai fatan ya ci gaba da zama abin koyi ga sauran shugabanni a jihar Kano.

By ukarofi