Kamfanonin lantarki sun sanya mitoci 70,888 ga sabbin kwastamomi a Agusta – NERC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta ƙasa (NERC) ta bayyana cewa Kamfanonin Rarraba Wuta (DisCos) sun sanya mitoci ga aƙalla sabbin abokan ciniki 70,888 a watan Agusta 2025.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton “Metering Factsheet” na watannin Yuli da Agusta 2025, wanda aka wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin a Abuja.

A cewar rahoton, sabbin mitocin da aka sanya a watan Agusta sun ragu idan aka kwatanta da 76,783 da aka saka a watan Yuli, alamar ci gaba a ƙoƙarin samar da mitoci a cikin masana’antar wutar lantarki ta Nijeriya (NESI).

Rahoton ya nuna cewa adadin masu amfani da wuta da ke da rajista a faɗin Nijeriya ya ƙaru daga miliyan 11.89 a watan Yuli zuwa miliyan 11.96 a watan Agusta 2025.

“Daga cikin wannan adadi, an riga an sanya wa abokan ciniki miliyan 6.58 mitoci, wanda hakan ke nuna ƙimar masu mita ya ƙaru zuwa kashi 55.01%, idan aka kwatanta da kashi 54.71% a watan Yuli,” inji rahoton.

Hukumar ta ce, waɗannan alƙaluman na nuna cewa ana samun ci gaba a hankali wajen rage gibin masu amfani da wuta da ba su da mita, da kuma inganta gaskiya da daidaito wajen biyan kuɗin wuta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa NERC kwanan nan ta amince da ware naira biliyan 28 ga kamfanonin wutar lantarki, domin siye da girka mitoci ga abokan cinikin da ke cikin rukunin Band A da Band B a yankunansu.

A cewar hukumar, kuɗin da aka ware ƙarƙashin ‘Tranche B na tsarin Meter Asset Financing (MAF)’, za su taimaka wajen rufe giɓin mitoci ga duka abokan ciniki da ke Band A, tare da hanzarta kammala girka mitoci ga waɗanda ke cikin rukunin Band B.

By ukarofi