
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya taya murna ga Mai bada Shawara na Ƙasa akan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu bisa cikarsa shekaru 65 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan mutanen da suka samar da gyara a Nijeriya bisa la’akari da gagarumar gudumawarsa ga ci-gaban ƙasa.
Ribaɗu, wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne kuma shugaba na farko a Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), a yau 21 ga watan Nuwamba, 2025 ya ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
A wani saƙon taya murna daga Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya yaba wa Ribaɗu a matsayin na gogaggen masanin harkar tsaro da jajircewa, wanda ya sadaukar ga adalci a cibiyoyin ƙasa, lamarin da ya haifar wa tsarin gwamnati sauyi.
Tinubu ya tunatar da hidimar Ribaɗu a EFCC musamman ganin yadda ya mayar da hukumar ginshiƙi wajen tabbatar da gaskiya da adalci da kiyaye dokar ƙasa.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ƙoƙarin Ribaɗu na yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, wanda ya taimaka wajen saita akalar shugabanci bisa ƙwarewa wajen yaƙar ayyukan rashawa a ofisoshin gwamnati.
Kazalika, Tinubu ya ce Ribaɗu har yanzu yana taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ƙasa kariya musamman duba da yadda take fuskanta ƙalubalen tsaro a sassanta.
